Coronavirus: Mawaƙiya Madonna ta kamu da cutar

Madonna

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mawakiyar, mai shekara 61, ta bayar da tallafin $1m domin samar da riga-kafin cutar korona.

Shahararriyar mawakiyar nan ta Amurka, Madonna, ta ce ta yi fama da cutar korona lokacin da ta yi tafiya zuwa wasu kasashen duniya.

A sakon da ta wallafa ranar Laraba a Instagram, ta ce ta harbu da cutar ne lokacin da ta yi balaguro na kasashen duniya mai suna Madame X.

Sai dai ta ce yanzu haka lafiyarta kalau amma dai gwajin da aka yi mata a baya ya nuna cewa tana da garkuwar jiki ta Covid-19 a cikin jininta.

"Idan gwaji ya gano cewa kana da garkuwar jikin, hakan yana nufin ka taba KAMUWA da cutar kuma na yi fama da rashin lafiya a kusan karshen balaguron da na yi zuwa Paris mako bakwai da suka wuce tare da 'yan rakiya ta, amma a lokacin mun yi tsammani mura ce mai zafi ta kama mu," in ji sakon da mawakiyar ta wallafa a Instagram, tana mai cewa yanzu dukkansu sun samu sauki kuma lafiyar lau.

Madonna ta katse balaguron da take yi bayan gwamnatin Faransa ta haramta gudanar da dukkan tarukan jama'a.

Mawakiyar, mai shekara 61, ta bayar da tallafin $1m domin samar da riga-kafin cutar korona.