Yadda wata mata 'ta daba wa mijinta wuka' a Nassarawa

Gwamnan jihar Nassarawa

Asalin hoton, KNSG

Hukumar tsaron farin kaya da kare al'umma ta Najeriya wato NSCDC, ta ce ta kama wata mata da ake zargi da kashe mijinta ta hanyar daba masa wuka a jihar Nasarawa.

Kwamandan hukumar a jihar ta Nasarawa Dr Muhammad Gidado Fari ya ce lamarin ya faru ne a ranar Talata, kuma tuni suka kammala bincike, inda daga bisani za su gurfanar da ita a gaban kuliya.

Dr Muhammad ya ce " mun samu wata da ta kashe mijinta inda ta daba masa wuka a kirji a kan zuciya. Ita da kanta ta fadi cewa ta caka masa wutar inda mutumin ya mutu."

Ya kara da cewa "mun mika ta ga likitoci domin yin bincike ko tana da wani ciwo na tabin hankali, inda gwajin ya nuna lafiyarta kalau.Mun kuma nemi iyayenta da 'yan uwanta domin tambayar su ko tana da tabin hankali inda su ma suka ce lafiyarta lau."

To sai dai hukumar ba ta yi bayani ba dangane da yanayin da matar da ake zargi ta aikata al'amarin.