Coronavirus: Abinci biyar da ke kare garkuwar jiki

Mangoro yana inta garkuwar jiki

Asalin hoton, Getty Images

Masana ilimin abinci sun bayyana cewa akwai bukatar mutane su rika shan cin nau'in abinci da 'ya'yan itace domin inganta garkuwar jikinsu.

Masanan sun ce cin wadannan na'ukua na abinci zai yi tasiri sosai a jikin mutum ta yadda zai ba shi kariya daga cututtuka irin su cutar korona.

Hajiya Zainab Ujudud Shariff, wata masaniyar abinci da tsarin amfani da shi ta shaida wa BBC nau'ukan abincin da suka kamata a rika ci domin inganta garkuwar jiki:

Zogale

Cin zogale da koren tattasai da kuli-kuli ko kuma tafasa shi a yi sirace da shi sannan a sha ruwansa. Kazalika za a iya mayar da shi gari sannan a rika sanya shi a cikin shayi ana sha. Binciken kimiyya ya gano cewa zogaye yana gyara garkuwar jiki.

Asalin hoton, Getty Images

Zobo

Shan zobon ruwan da aka hada da citta da kanimfari ba tare da suga da yawa ba yana gyara garkuwar jiki.

Bayanan sauti

'Ya'yan itace biyar da ke kare garkuwar jiki

Mangoro

Mangoro yana dauke da sinasarin phytonutrients da phytochemicals da kuma anti-oxidantant property. Suna karfafa garkuwar jiki. Don aka yana da matukar amfani a wanke mangoro kafin a sha. Yana da kyau a hada mangoro da goba da kankana wuri guda ta hnayar yanka su sanna a sha su lokaci guda.

Asalin hoton, Getty Images

Kindiro

Kindirmo musamman wanda aka tatso daga jikin saniya kai tsaye yana ingata garkuwar jiki. Amma babu laifi idan mutum ya yi amfani da kindirmo dan kanti.

Citta da kanimfari

Citta da kaninfari suna gyara garkuwar jikin mutum. A sanya su a cikin ruwan zafi a sha su.