Coronavirus: Matar da aka tofa wa yawu ta mutu sanadin cutar

Belly Mujinga

Asalin hoton, Family handout

Bayanan hoto,

Ma'aikaciyar a ofishin sayar da tikitin Belly Mujinga ta mutu ne sakamakon cutar korona a watan Afrilu

Wata mai sayar da tikitin jirgin kasa ta mutu bayan wani mutum da ya yi ikirarin yana da cutar korona, ya tofa mata yawu.

Matar Belly Mujinga, na da shekara 47, kuma tana da wasu kwantattun cutukan numfashi, inda take aiki da tashar jirgin kasa ta Victoria a London lokacin da aka tofa mata yawun a watan Maris, tare da wata abokiyar aikinta.

Bayan 'yan kwanaki da faruwar lamarin dukkan matan sai suka kamu da rashin lafiya sakamakon kwayar cutar.

'Yan sandan Sufuri na Burtaniya sun ce sun kaddamar da bincike don bin sawun mutumin da ya tofa musu yawun.

Mrs Mujinga tana gaban harabar tashar Victoria ne ranar 22 ga watan Maris lokacin da mutumin da ake zargi ya tunkare ta.

Mijin mamaciyar Lusamba Gode Katalay ya ce mutumin ya tambayi matarsa abin da take yi da kuma dalilin da ya sa take tsaye a wurin.

Ya kara da cewa "Ta fada masa cewa ita ma'aikaciya ce, daga nan sai ya fada mata cewa yana dauke da kwayar cutar korona kuma ya tofa mata yawu".

An kai Misis Mujinga asibiti ne ranar 2 ga watan Afrilu, inda aka sanya mata na'urar taya numfashi. Amma ta mutu bayan kwana uku a can, in ji kungiyar ma'aikatan sufuri masu karbar albashi (TSSA).

Asalin hoton, Family handout

Bayanan hoto,

Belly Mujinga leaves behind an 11-year-old daughter

Mai magana da yawun Fira ministan Burtaniya, ya bayyana wannan hari a kan muhimmiyar ma'aikaciyar da cewa "abin kyama ne".

Mijin marigayiyar ya ce ya kira matarsa ta hanyar manhajar bidiyo lokaicn da take kwance a asibiti, amma tun daga nan bai sake jin komai daga gare ta ba.

"Na dauka kila tana ta barci ne, amma sai likita ya kira ni ta wayar tarho yana bayyana min cewa matata ta rasu," in ji shi.

"Mutuniyar kirki ce, kuma uwa ta gari, ga ta salihar matar aure. Mace ce mai nuna kulawa."

Mutum goma ne suka halarci jana'izar Misis Mujinga, ciki har da 'yarta mai shekara 11.

Babban sakataren kungiyar Manuel Cortes ya ce: "Mun kadu tare da gigituwa kan mutuwar Mujinga Belly. Tana daya daga cikin ma'aikatanmu na gaba-gaba da dama da suka mutu sakamakon kwayar cutar korona."

Bayanan hoto,

British Transport Police said an investigation had been launched following the incident at Victoria station

Kungiyar ta kuma ce akwai "kwakkwarar ayar tambaya game da mutuwarta".

'Tragic incident'

Kamfanin da Misis Mujinga ke yi wa aiki, Govia Thameslink Railway (GTR), ya ce yana "daukar duk wasu zarge-zarge da gaske" kuma yana gudanar da bincike kan duk wani ikirari da aka yi.