Coronavirus a Kano: Mutum 33 sun mutu, 27 sun sake kamuwa a rana guda

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatar lafiya ta jihar Kano a Najeriya ta ce ya zuwa daren Talata, an samu karin mutum 27 da suka kamu da cutar korona a jihar.
Hakan na nufin adadin mutanen da ke dauke da cutar a Kano ya kai 693, tun bayan bullar cutar a jihar, sai dai kuma an sallami mutum 74, inda 33 suka riga mu gidan gaskiya.
Jadawalin jihohin da cutar ta bulla da hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya, NCDC ta fitar ya nuna Kano ce ta biyu a yawan masu fama da cutar bayan Legas mai mutum 1,990 da Abuja babban birnin kasar inda ake da mutane 360.
A ranar 11 ga watan Afrilu ne hukumomi a Kano suka sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar kuma tun daga wannan lokacin aka rika samun karuwar mutanen da annobar ta shafa, kuma ci gaba da gwaje-gwaje a jihar bayan an sami tsaiko ya sa aka samu karuwar yawan wadanda ke dauke da cutar.

Asalin hoton, Getty Images

Alkaluman mutum 27 da hukumar NCDC ta fitar a daren Talata na wadanda suka kamu da cutar na nuni da yadda annobar ke sama ta kuma yi kasa a jihar ta Kano.
A yanzu dai cutar na kara bazuwa a jihohin da ke makwabtaka da Kano - Katsina na da mutum 208 sai Jigawa mai mutum 118, Bauchi na da 190 yayin da Kaduna kuma ta ke da mutum 111.
A cewar sanarwar da hukumar NCDC ta fitar a Twitter, zuwa daren Talatar, mutum 4,787 ne suka kamu a jihohi 34 har da Abuja. Daga cikin adadin, 959 sun warke har ma an sallame su daga inda ake kulawa da su.
Sai dai adadin wadanda suka mutu sakamakon cutar ya karu, inda jimilla mutane 158 suka riga mu gidan gaskiya.