Wani mutum ya shafe mako takwas a filin jirgin sama saboda coronavirus

MaNOJ MUNDACKAL

Asalin hoton, MaNOJ MUNDACKAL

Bayanan hoto,

Mista Edgard Ziebat ya shafe kusan mako takwas a filin jirgin saman Delhi

Wani Bajamushe wanda ya shafe mako takwas a ginin wani filin jirgin sama na kasar Indiya ya sami tafiya zuwa birnin Amsterdam.

Mutumin ya makale ne a filin jirgin saman bayan da Indiya ta dakatar da dukkan zirga-zirgan jiragen sama domin dakile bazuwar cutar korona.

Mista Edgard Ziebat ya sauka a babban filin jirgin sama na Delhi daga birnin Hanoi ranar 18 ga watan Maris, inda ya sa ran shiga wani jirgin da zai wuce da shi zuwa Santanbul bayan wasu sa'o'i.

Amma sai kwatsam ya taras da an soke jirgin da zai shiga - har ma da sauran jirage da fasinjoji masu dama ke jira.

Daga nan ne fa ya makale domin gwamnatin Indiya ta hana shi shiga cikin birnin saboda rashin takardar izini wato biza.

Ya kuma yi rashin sa'ar shiga wani jirgin da Jamus ta aika da shi can domin kwashe 'yan kasarta.

Asalin hoton, MaNOJ MUNDACKAL

Kafofin watsa labarai na kasar ta Indiya sun rika kwatanta shi da wani mutum da shi ma ya makale a wani fim da Tom Hanks ya fito cikinsa mai suna The Terminal.

Amma masu kula da filin jirgin saman na Delhi sun ce sun rika ba shi abinci, da sabulun wanka da na wanki da kuma wani dan karamin gado.

Ya dai shafe makonni a filin jirgin yana karanta litttatafai da magana da abokansa ta wayar tarho.

Asalin hoton, MaNOJ MUNDACKAL