Buhari ya yi tir da hare-haren 'ramuwar gayya' a Kajuru

Buhari

Asalin hoton, Presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tir da abin da ya bayyana "hare-haren ramuwar gayya a yankin karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.

A wani sakon tiwita da ya wallafa cikin daren Talata, Shugaba Buhari ya ce ba daidai ba ne kisan gilla da sunan ramuwar gayya.

A cewarsa karuwar hare-hare da na ramuwar gayya kan mutane tsakanin al'ummomin Fulani da na Addara cikin yankunan Kajuru, abin Allah wadai ne,

Jihar Kaduna dai ta yi kaurin suna game da yawaitar hare-haren masu satar mutane don neman kudin fansa da 'yan fashin daji da kuma na kabilanci.

Jaridar Premium Times da ake wallafawa a intanet ta ruwaito 'yan sanda a jihar Kaduna na cewa wasu mutane da ake zargi 'yan fashin daji ne sun kashe mutum 15 a kauyen Gonar Rogo na Kajuru.

Ta ambato mai magana da yawun 'yan sandan, Mohammed Jalige na cewa rundunarsu ta samu wani kiran waya a gigice ta hanyar baturen 'yan sanda na Kajuru cewa rukunin wasu mutane dauke da makamai a kan babura sun yi wa kauyen Gonar Rogo tsinke.

"Maharan sun rika harbi ba-ji-ba-gani ta hanyar far wa mazaunan kauyen, lamarin da ya kai ga hallaka mutum 15 tare da jikkata wasu biyar," in ji shi

Ya ce a daidai lokacin da suka shiga farautar maharan da suka tsere, sun kuma kai gawawwakin mutanen da aka kashe tare da jikkatawa zuwa asibiti.

A cewarsa, tuni kuma aka tura karin 'yan sanda zuwa yankin "don bincike da gudanar da sintiri da nufin hana sake karya doka da oda ko kuma harin ramuwar gayya da kuma kama wadanda suka tafka aika-aikar."

Shi dai Shugaba Buhari ya ce daukar gabarar yin gaban kai maimakon barin dokar kasa ta yi aikinta shi ne musabbabin wadannan kashe-kashe da hare-haren ramuwa.

Don haka ya ja kunnen al'ummomin biyu cewa babu wani mutum da yake da damar yanke wa kansa/ta hukunci