Coronavirus: WHO za ta soma koyar da darusa da Hausa

Bayanan sauti

Darussa kan cutar korona da Hausa

Latsa hoton da ke sama domin jin bayanin Dr Nasir Sani Gwarzo

Hukumar Lafiya ta duniya, WHO, ta ce za ta soma koyar da darusa kan cutar korona cikin harshen Hausa, da Swahili da kuma Amharic.

Shugaban Hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Alhamis.

A cewarsa, za a soma koyar da darasin, mai taken 'Intro to #COVID19' a turance, wato 'Gabatarwa kan cutar korona' a shafin intanet.

Mr Ghebreyesus ya ce harsunan uku za su bi sahun harsuna 13 da tuni aka soma amfani da su wajen koyar da darusan.

Ya ce: "Muna mai farin cikin sanar da ku cewa #OpenWHO ta kaddamar da shiri mai taken 'Gabatarwa kan cutar korona' a sabbin harsuna uku: Amharic (አማርኛ), Hausa & Swahili - yanzu kenan harsunan da ake darasin da su sun kai 16. Za a kawar da cutar korona a fadin duniya ne kawai ta hanyar yaɗa ilimi. Dukkanmu za mu iya yin hakan.!

Shugaban na WHO ya ce duk mai son shiga darasin zai iya latsa nan.

Alkaluma sun nuna cewa mutum tsakanin miliyan 100 zuwa 150 ne suke magana da harshen Hausa, abin da ya sa ya zama harshen gida da aka fi magana da shi a Afirka.