Coronavirus: Me ya sa ya kamata 'yan Afirka su yarda da gwajin riga-kafin korona?

  • Daga Anne Mawathe
  • Edita kan harkokin Lafiya a Afirka, BBC News
A generic photo of a masked nurse holding up a vaccine

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masana sun yi gargaɗin cewa idan Afirka ta juya wa gwajin riga-kafin korona baya ƙasashen duniya za su iya ware ta

An yi ta yaɗa labarai masu tayar da hankali game da allurar riga-kafin annobar cutar korona da aka ce za a yi gwajinta a Nahiyar Afirka.

Sai dai kuma masana sun yi amanna cewa yana da mahimmanci idan Afirka ta shiga aka dama da ita, suna masu cewa rashin yin hakan ka iya kawo tsaiko ga yunkurin samar da riga-kafin ga duniya baki ɗaya.

Tun a watan Maris ne shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa "duniya ta dunƙule wuri guda" wurin neman maganin cutar da ake yi wa laƙabi da Covid-19.

Ganbin ncewa har yanzu ba a samu maganimnta ba, riga-kafi zai taka muhimmiyar rawa wurin bayar da kariya tare da kula da masu cutar idan sun kamu, a cewar WHO.

Za ta ƙarfafa garkuwar jikin dan Adam ta yadda zai yaƙi cutar.

Yaya riga-kafi ke aiki:

  • Yana ƙarfafa garkuwar jiki ta hanyar ƙwaiƙwayon cutar
  • Hakan na taimaka wa garkuwar jiki wurin fahimtar cutar da kuma yadda za ta ɓullo mata
  • Riga-kafi kan ɗauki tsawon lokaci kafin a same ta, ko ma shekaru
  • Riga-kafin Covid-19 za ta bayar da damar cire dokar kulle da kuma sassauta dokar nesa-nesa da juna

Ya zuwa yanzu an fara gwajin riga-kafi ɗaya a Afirka ta Kudu - sannan ana jiran umarnoin fara gwakjin wani a Kenya.

Sai dai harkokin gwajin na cike da ce-ce-ku-ce.

Yayin da aka saba ƙyamar kowanne irin riga-kafi a Afirka, yanzu kuma ce-ce-ku-cen wariyar launin fata ce kan gaba.

'Tunanin mulkin mallaka'

Duk wannan ya fara ne lokacin da wasu likitoci a Turai da Australia suka fara tunanin ko riga-kafin tarin fuka zai yi aiki a kan cutar korona.

Yayin da suke muwara a talabijin, dukkansu sun yi amannr cewa ya kamata a yi gwajin maganin a Afirka.

Kalaman da daktocin suka yi amfani nda su ya janyo zazzafar muhawara da Allah-wadai.

"Abin kunya ne a ji irin waɗannan kalamai a cikin ƙarni na 21 daga masana kimiyya," in ji Dr Tedros, shugaban WHO wanda ɗan ƙasar Habasha nbe wato Ethiopia.

"Muna tabbatar muku cewa hakan ba za ta saɓu ba. Wajibi ne wannan tunanin na mulkin mallaka ya tsaya haka."

Sauran taurari daga Afirka ma sun tofa albarkacin bakinsu a wannan magana, ciki har da tsohon ɗan ƙwallon Ivory Coast Didier Drogba da na Kamaru Samuel Eto'o - waɗanda da ma aka saba yi musu kalaman wariya a filayen wasanni.

Fushin da mutane ke nunawa yana da tushe, domin kuwa akwai hujja cewa wasu kamfanonin magani sun sha yin gwajin magani a Afirka ba tare da mutunta haƙƙin dan Adam ba ko kuma bin dokoki.

Kuɗin fansa

Kamfanin Pfizer ya taɓa yin gwajin wata mamugunciyar ƙwaya a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya a shekarar 1996.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Gomman yara ne suka samu nakasa sakamakon gwajin ƙwayar da Pfizer ya yi a Kano

Bayan tsawon lokaci ana tafka shari'a, kamfanin ya biya wasu iyaye diyyar yaransu da aka gwada maganin a kansu yayin wata annobar cutar sanƙarau a Kanon.

Yara 11 ne suka mutu sanna wasu gommai suka samu lalurori daban-daban. Hakan ya jawo tambayoyi iri-iri cewa ko ma an nemi izinin jama'a kafina a yi gwajin a kansu.

Fiye da shekara 20 kenan, sai dai wani ƙwararre a ƙasar Uganda ya ce yanzu al'amura sun sauya.

"Yanzu ɗaiɗaikun mutane na kulka da kansu," in ji Dr Kyobutungi, shugabar cibiyar African Population and Research Center (APHRC) a hirarsa da BBC.

"Idan masanin kimiyya ne kai da ke samar da riga-kafi, ba za ka so a ce bayan wasu 'yan shekaru riga-kafijnka na kashe mutane ba.

"Saboda haka mutane na ɗari-ɗari da kimarsu yanzu saboda suna yawan sadaukar da ayyukansu."

Ta ƙara da cewa a gwamnatance ma yanzu akwai sa ido - ƙasashe na da hukumomi da ke sa ido kamar National Council of Science and Technology ta Uganda.

Shi ma Richard Mihigo, wani mai sa ido kan riga-kafi na WHO a Afirk, ya yarda cewa an samu sauyi yanzu.

"Yayin gwajin, akwai sa ido da kuma tallafi ta yadda da wuya a jefa 'yan Afirka cikin haɗarin magungunan da ba su da inganci."

Ya ƙara da cewa waɗanda suka yi gwajin ba a ba su damar shiga harkokin sayar da maganin a kasuwa.

'Annobar labaran ƙarya'

Irin waɗannan maganaganu na cin karo da ɗaruruwan labaran ƙarya da ake yaɗawa a intanet da kafafen yaɗa labarai cewa za a yi gwajin magani kan baƙaƙen fata da zummar kashe su.

Misali, akwai wani labari da aka yaɗa cewa yara bakwai suyn mutu a ƙasar Senegal bayan an ba su wani riga-kafin cutar korona, abimn da ya jawo tayar da jijiyoyin wuya a Facebook.

Shekaru ba tare da isassun kuɗi ba

Sai dai abin da ake mantawa shi ne yadda kiwon lafiya a Afirka ya daɗe ba tare da samun kyakkyawar kulawa ba.

Wannan kuwa duk da alƙawarin da shugabannin nahiyar suka yi a shekarar 2001 na ware aƙalla kashi 15% na kasafin kuɗin kasashensu domin bunƙasa ɓangaremn lafiyar.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Cibiyar Pasteur a Senegal na yin wani bincike kan cutar korona

Zuwa yanzu ƙasa biyar ne kacal suka cimma wannan fatan cikin 54 da ke nahiyar - wanda ya jawo koma-baya a ɓangaren binciken lafiya na tsawon shekaru.

Afirka na da ƙwarewa iri-iri amma ma'aikatanta kan gwammace su tafi aiki wasu nahiyoyi saboda ƙarancin kuɗaɗen aiki - hakan na nufin matsalolin binciken lafiya a Afirka ba a fiya yin maganinsu ba.

Waɗanda suka zauna kuma ba sa iya haɗa tarukan ƙara wa juna sani, yayin masu ɗaukar naiyin irin waɗannan shirye-shiyen sun fi son zuwa ƙasashen da suke da kayan aikin lafiya - shi ya sa aka fi yin gwaji a Masar (Egypt) da Afirka ta Kudu.

Kazalika an fi yin gwajin a ƙasashe masu arziki kamar na Turai da Arewacin Amurka, saboda haka ba a fiya damuwa da yadda ya kamata a yi amfani da magungunan a Afirka ba.

Gabashin Turai da Asiya da Gabas ta Tsakiya ma ba a fiya kula da su wurin yin gwaji ba - duka da cewa al'mura sun sauya a yankunan matuƙa cikin shekaru.

'Za a iya yi babu Afirka'

Masana sun yi ta gargaɗin cewa idan har ana son kawo ƙarshen wannan annoba to dole ne a samar wa duniya bakmi ɗaya riga-kafi.

Suka ce idan Afirka ta sake ta juya baya ga gwajin magungunan to za a iya ware ta.

Dr Kyobutungi ta ce: "Ba zai yi kyau ba a ce an yi gwajin magani a Birtaniya misali, sannan a akwo shi Afirka saboda muna bambancin yanayi da bambancin halittunmu, wanda ka iya shafr yadda maganin zai yi aiki.

"Muna da mabambantan abubuwa; muna kuma da sauran cutuka ma. Misali, akwai masu cutar HIV da yawa."

Sai dai abin da ya fi damunta shi ne, ko ma dai ya aka yi sai an nuna wa Afirka wariya saboda nahiyar na da matsalolin gwajin cutar korona "yayin da ƙasashe ke mayar da kayan yaƙinsu sannan ba sa son sayen kayan aiki".

"Saboda babbar matsalar a nan ita ce, ga riga-kafin nan amma ƙasashe masu arziki za su saye shi duka su bar Afirka," in ji ta.

Yayin da ake ci gaba da yin gwajin riga-kafi a faɗin duniya, shugabanni da masana sun rubuta wata wasiƙa suna kira da a samar da riga-kafi "ta jama'a".

An ambato Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa a cikin wasiƙar yana cewa Afirka na buƙatar riga-kafi "cikin gaggawa kuma ta kyauta ga kowa da kowa".

"Bai kamata a mayar da wani ƙarshen layin karɓar riga-kafi ba saboda nahiyarsa da yake zaune ko kuma arzikinsa," in ji shi.