Coronavirus a Najeriya: Yadda cutar ta jefa almajirai cikin mawuyacin hali

Kids from different district of Nigeria learn to read and memorize the verses of the Quran written with ink on wooden panels at a boarding school in Jimeta, Nigeria on December 08, 2014.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana kai yaran da basu da galihu makarantun kur'ani a arewacin Najeriya

Wasu 'yan siyasa masu karfin fada-a-ji a Najeriya suna kokarin dakatar da tsarin makarantun allo bayan almajirai sun tsinci kansu a tsaka da cutar korona, kamar yadda wakilan BBC Nduka Orjinmo da Mansur Abubakar suka ruwaito.

Dubban yaran da ke zuwa makarantun allo a arewacin Najeriya ne ake kamawa ana zuba su a manyan motoci don mayar da su jihohinsu na asali, a wani mataki da gwamnatocin jihohin suka dauka na dakile cutar korona a yankin nasu.

An haramta zirga-zirga daga jiha zuwa jiha, amma ana barin manyan motocin dauke da wadannan yaran su hau manyan hanyoyin jihohin domin mayar da su kauyukansu.

Kusan duka jihohi 19 da ke yankin arewacin Najeriyan na aike wa da yaran jihohinsu na ainihi, yayin da kuma su ma suke karbar nasu da ke wasu jihohin.

Wannan zai iya zama musayar almajirai mafi girma da jihohin suka yi tsakaninsu a kasar da ta fi yawan al'umma a Afrika.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Ana samun yara da dama da ke yawon bara a manyan titinan Kano

Babu wanda ya san yawan wadannan yaran - jihar Kaduna kawai ta mayar da almajirai 30,000 daga cikinsu.

Abin da babu wanda ya sani shi ne, daruruwan yaran nan sun kamu da wannan cuta ta korona.

'Sun yi watsi da gargadin'

Da komawar yaran jihohinsu an killace da yawa daga cikinsu wadanda aka gwada kuma aka tabbatar suna dauke da cutar.

Sakamakon ya yi matukar jan hankali - lokacin da aka gwada 169 aka ga 65 cikinsu na dauke da cutar korona a Kaduna, da kuma 91 da aka samu da cutar cikin 168 da aka gwada a Jigawa.

Asalin hoton, Jigawa state government

Bayanan hoto,

Har yanzu ba a san ta yaya yaran ke kamuwa da wannan cuta ba

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A Gombe an samu yara 48 dauke da cutar bayan an yi musu gwaji. A Bauchi, yara bakwai aka samu da cutar cikin 48 da aka mayar.

Har yanzu ana jiran sakamakon daruruwan gwajin da aka bayar, kuma akwai dubban almajiran da har yanzu ba a yi musu gwajin ba - Najeriya dai na fuskantar suka kan karancin kayan gwajin cutar korona.

Shugaban kwamitin kar-ta-kwana na kasar a an cutar, Boss Mustapha, ya yi gargadin cewa mayar da yaran jihohinsu zai iya jawo yaduwar cutar a arewacin kasar, sai dai gwamnonin jihohin sun yi watsi da wannan gargadi.

Sun dauki wannan annoba a matsayin wata dama da za su kwashe almajiran da ke zaune a makarantun allo, tsarin da aka jima ana bi a arewacin kasar.

"Muna ta kokarin nemo hanyar da za mu kawo karshen wannan tsarin, saboda ba ya taimaka wa yara da komai. Ba ya taimakawa arewacin Najeriya, ba ya taimaka Najeriya. Don haka, ya kamata a kawo karshensa kuma wannan ne lokacin da ya dace," in ji gwamnan jihar Kaduna Nasir el-Rufa'i.

Ya kara da cewa zai fi kyau a bai wa almajiran "ilimin zamani maimakon barinsu haka suna ɓata rayuwarsu, suna yawo a kan titi suna barar abin da za su ci".

"A nan Kaduna mun gama da tsarin karatun almajirai" a cewar el-Rufa'i

Mafi yawan almajiran yara ne da suka fito daga gidajen masu karamin karfi, suna tafiya su yi karatu na tsawon shekara biyar zuwa 10 a makarantun allon karkashin malamin makarantar.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Musulmai sun yi amannar cewa haddar Kur'ani sai wanda Allah ya zaba

Kimanin yara miliyan 10.5 a Najeriya da ke tsakanin shekara biyar zuwa 14 ba sa zuwa makaranta, kamar yadda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya, Unifec ya bayyana.

Unicef ba ta kallon almajirai a matsayin yaran da ke zuwa makaranta don haka adadinsu ya fi yawa cikin wadannan yara.

Yaran da ake tura wa bara kan tituna

Irin wadannan makarantu na almajiri na daukar yara har 'yan kasa da shekara biyar, kuma kowanne cikinsu yana bai wa malamansu kudin da suka kai naira 100 ko wacce Laraba, wanda ake daukar Alhamis da Juma'a a matsayin ranakun karshen mako.

Malaman na cewa ana amfani da kudaden ne wajen tafiyar da makarantar, ba wai sa kudin suke a gaba su cinye ba.

Mafi yawan almajirai ba su da kudin da za su biya wannan naira 100 ta mako har sai sun fita sun yi bara kan tituna. A wasu lokutan sukan yi ayyukan da suka fi karfinsu ga wasu iyalan domin samun abinci da tufafi.

Suna rayuwa ne cikin kazanta, sukan dauki kwanaki babu wanka, duk da cewa addinin musulunci ya bayar da muhimmanci kan tsafta.

Su kansu malaman makarantar talakawa ne, ba kuma su da wata kwarewa. Suna kokarin koyarwa kuma suna aikin gona. Wasu yara na zuwa gonar su taimaka, kuma ba a ba su komai haka suke komawa gida.

Koyarwar addinin Musulunci game da tsafta:

  • Tsafta rabin imani ce
  • Wanke hannu kafin da kuma bayan an ci abinci
  • Wanke hannu bayan fitowa daga banɗaki
  • Ana yi alwala gabanin ko wacce sallah a kullum
  • Ana wanka na musamman kafin sallar Juma'a da ake yi duk mako
  • Ana wanke mutum bayan ya mutu, amma wasu malaman na ganin babu wata damuwa idan ba a yi wankan ba saboda halin da ake ciki

An rufe duka makarantun allo lokacin da gwamnonin yankin suka ba da sanarwar rufe wuraren tarukan jama'a a krshen watan Maris, amma saboda babu wurin zuwa almajiran na ci gaba da bara kan tituna.

A daidai lokacin da gwamnonin ke tsoron yaran za su iya kamuwa da cutar, kuma su yaɗa ta ga daruruwan mutanen da suke mu'amala da su a ko wacce rana - don haka aka yanke shawara a tura su gida.

Bayanan hoto,

Tsohon almajiri Imrana Mohammed da ya zama dan kasuwa

Sai dai lokaci ya kure.

Babu wanda ya san ta yaya waɗannan yaran suka kamu da wannan cuta, sai dai Imrana Muhammed wanda tsohon almajiri ne ya ce "watakila sun kamu ne ta hanyar haduwa da baki yayin kokarin karbar sadaka".

Muhammed wanda ke kasuwanci sayar da man fetur yanzu, ya ce ya yi almajirci shekara 14 da ta gabata, yayi aikin a gidaje da yake samu kimanin naira dubu da da dari biyar kan ya samu abin da zai ci.

An ta tattauna yadda za a kawo karshen wannan tsarin karatu a baya a yankin inda al'amuran da suka shafi addini ke da matukar muhimmanci. Masu goyon bayan tsarin na zargin wadanda ke son a sauya tsarin da kokarin dakatar da ilimin addini.

Fata na gari

Tsohon shugaban ƙasar Goodluck Jonathan, wanda kirista ne da ya fito daga yankin kudancin kasar, ya kashe biliyoyin naira don gina makaratun almajiri a arewacin kasar wadanda za su rika aiki da tsarin koyarwar addinin musulunci.

Amma wanda ya gaje shi, Muhammadu Buhari da ya fito daga yankin arewan ya nemi da a haramta gudanar da tsarin, ya kuma mika gudanar da makarantun hannun gwamnonin jihohi don tafiyar da su. An watsar da makarantu da dama kuma yaran sun koma barace-barace kan tituna.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yara da dama na amfani roba don neman abinci

Wasu iyayen kamar Shafi'u Ya'u ba sa son wannan tsarin ya ruguje, "saboda hanyar tsira ce".

Ya shaida wa BBC cewa ɗansa mai shekara 15 yanzu na almajiranci a Kano, inda ake wa kallon nan ne cibiyar karatun allo a Najeriya, ba dai duka yaran ba ne aka mayar gidajensu musamman ma a Jihar Kano.

"Wannan ce shekarar shi ta biyu kuma ina sa ran nan da shekara biyar zai dawo gida da tarin ilimi mai yawa na Kur'ani da addini," in ji malan Ya'u.

Amma ba kowa ne ke da irin wannan ra'ayin ba.

Sheikh Abdullahi Garangamawa
The almajiri system, as it is today, is nothing but slavery"
Sheikh Abdullahi Garangamawa
Senior Muslim cleric in northern Nigeria

Sheikh Abdullahi Garangamawa shi ne babban lilmamin masallacin Jafar Adam a Kano da ke arewacin Najeriya, ya shaida wa BBB cewa an lalata tsarin karatun allo ne.

"Wannan tsarin ya zama kamar bautar da yara a yau, ya kamata gwamnati ta dakatar da tsarin cikin hanzari ta daina jan kafa.

"Wadannan yaran da ake aikowa daga kauyuka ba karatu suke ba yanzu - da yawansu na zama mutanen kawai wasu kuma 'yan bangar siyasa," in ji shi.

Wannan ba karamin tsattsauran ra'ayi ba ne a wajen malaman da ke tafiyar da irin wannan tsarin a arewacin Najeriya, amma da wahala gwamnati ta samu nasarar hakan matukar ba ta kawo karshen talauci ba, da kuma samar wa iyayen yaran wani abu mai muhimmanci maimakon halin da suke ciki.