'Yan bindiga sun kashe mutum 8,000 a arewa maso yammacin Najeriya - ICG

Zamfara na cikin jihohin da wannan bala'i ya fi addaba.

Asalin hoton, Zamfara government

Bayanan hoto,

Zamfara na cikin jihohin da wannan bala'i ya fi addaba.

Kungiyar nan mai bincike kan tashe-tashen hankula a kasashen duniya, International Crisis Group, ta ce an kashe mutane fiye da dubu takwas a rikicin arewa maso yammacin kasar cikin shekaru 10.

Kungiyar ta ce rikicin ya raba fiye da dubu dari biyu da muhallansu a rikice-rikice da kuma hare-hare a yankin cikin shekaru kimanin goma.

A wani rahoto da ta fitar yau, Kungiyar ta ce kawo yanzu kokarin hukumomi ya gaza kawo karshen tashin hankalin, wanda ya fi shafar jihohin Zamfara da Sokoto da katsina da kuma Kaduna.

Ko a jiya rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kashe mutum a kalla goma sha biyar a jihar Zamafara.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya ba hukumomin tsaro izinin kai sabon farmaki babu kakkautawa kan 'yan bindiga a wuraren da suke.