'Yan bindiga sun kona gidan hakimin Dapchi

Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images

A Najeriya wasu Mahara da ake kyautata zaton mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari garin Dapchi inda rahotanni suka ce sun bude wuta wanda ya tilastawa mutanen garin tserewa zuwa daji.

Ba a san yawan adadin mutanen da harin maharan ya shafa ba a garin na Dapchi da ya sha fama da hare-haren Boko Haram.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa, mutanen sunzo ne da yammacin ranar Litinin 18 ga watan Mayu, 2020, inda suka bude wuta suna ta harbe-harbe.

Mutumin ya ce ' Ina cikin gida sai naji harbi abin da ya tsoratar dani ke nan sai na gudu zuwa bayan gari a can ne na hadu da mutane da dama da suma suka gudu".

Ya ce " Anan ne naji ana cewa ai maharan sun kona gidan hakimi, koda naje na ganewa idanuna sai na tarar sun kona gidan".

Mutumin ya ce kafin maharan su kona gidan hakimin sai da suka kwashi kayan sawa da na abinci, daga nan ne kuma sai suka sawa gidan fetur suka kona.

Ya ce " Koda maharan suka je gidan hakimin basu tarar da kowa ba domin duk mutanen gidan sun gudu da suka ji karar harbi".

Mutumin ya ce, shi dai bai ga gawa ko daya ba domin duk kusan mutanen garin sun gudu sun shiga daji da suka ji harbin farko, sai dai-daiku kawai suka rage a gidajensu.

Ya ce, daga baya sun ji labarin cewa sojoji sun shiga garin, amma kuma sai da maharan suka shafe kusan sa'a guda a cikin garin kafin jami'an tsaron su shiga garin.

Har yanzu dai jihohin da ke arewa maso gabashin Najeriya na ci gaba da fuskantantar hare-haren 'yan bindiga a lokuta da dama.

Matsalar tsaro a Najeriya matsala ce data ki ci taki cinyewa abin wasu ke ganin gazawar gwamnati wajen kawo karshen wannan matsala da ta addabi al'ummar kasar.