Coronavirus a Najeriya: Muna tufka jihohi suna warwarewa - Buhari

SHUGABA BUHARI

Asalin hoton, BUHARI SALLAU

Gwamnatin Tarayya ta nuna rashin gamsuwarta da yadda ake samun sabani tsakanin matakan da take dauka kan yaki da korona da kuma matakan da wasu jihohi ke dauka a nasu bangaren.

Wannan na zuwa ne bayan tsawaita dokar takaita zirga-zirga da gwamnatin ta yi a jihar Kano da mako biyu gaba.

A ranar Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari ya tattauna da wasu gwamnonn jihohi ta intanet kan batun yaki da cutar korona da kuma batutuwan da suka shafi tattalin arziki da tsaro.

Sai dai Shugaban Najeriya ya nemi hadin kan jihohin, inda ya ce gwamnatin Tarayya na tufka wasu jihohin na warwarewa.

A tattaunawarsa da BBC Malam Garba Shehu mai taimakawa shugaban kan harkokin watsa labarai ya shaidawa cewa abin takaici ne a ce gwamnati tana daukan matakan yaki da annoba amma ana samun matsalar hadin-kai.

Ya ce "ba wai zargi mu ke yi ba ko kushe, amma akwai bukatar a ce ana tafiya tare saboda idan matsaya ba ta zo guda ba, da wuya a yi nasara a yaki da korona".

Malam Garba, ya ce kwamitin da ke yaki da annobar na kasa na kokawa kan yadda matakan wasu jihohi ke warware nasarorin da ake samu akan annobar.

"Kamata ya yi kafin a dau kowanne irin mataki to a tuntube masana don neman shawarwari".

Kakakin dai ya ce ba wai ana ganin babu hadin-kai daga gwamnoni ba ne, sai dai lura da cewa kowacce jiha ita ke daukan nata matakin akwai bukatar take aiki da shawarwarin kwararru.

Wannan batu na Garba Shehu na zuwa ne sa'o'i da jihar Kano ta yiwa sabon umarnin shugaban kasa kan yaki da korona a jihar kwaskwarima.

Gwamnan Kano ya sassauta dokar kullen da gwamnatin Tarayya ta tsawaita da mako biyu, inda ya bada damar fita a ranakun Lahadi da Laraba da kuma Juma'a. Sannan za a gudanar da sallar idi da cigaba da sallar Juma'a.

Sai dai a lokacin da aka yi wa Garba Shehu tambaya akan matsayar fadar gwamnati kan mataki na Kano, ya amsa cewa fatansa shi ne a yi komai bisa cancanta da shawarwari kwararu domin lallai akwai bukatar hadin-kai

Ya ce ''idan ba a yi aiki tare ba to akwai matsala saboda shawo kan annobar zai yi wahala saboda yaki da korona ya shafi kowa, kama daga kan gwamnatin Tarayyar har zuwa jihohi''.

''Idan ba a yi aiki tare ba ma'ana a tashi tare a fadi tare, tufkar da ake yi to warwareta za a yi''

Asalin hoton, Facebook/Salihu Tanko Yakasa

Bayanan hoto,

Ganduje ya ce za ayi sallar Idi a Kano

Hikimar Ganduje

Mako na biyar kenan da Jihar Kano ke cikin dokar kulle ko da yake akwai ranakun da ake bai wa mutane damar fita domin cefane.

Al'ummar Kano sun yi ta dakon ji ko za a basu damar gudanar da bikin sallah, hakazalika malamai sun yi ta kiran a sassauta matakan da ake dauka domin ci gaba da salolin jam'i.

Gwamna Ganduje ya ce ya amince da shawarwarin da wasu malamai suka ba shi na bayar da izinin yin Sallar Juma'a da kuma Idi.

Kwamishinan yada labarai Jihar Muhammad Garba ya shaidawa BBC cewa suna sane da irin wahalhalun da al'ummar Kano suka shiga saboda zaman gida.

Saboda haka sun dau wadanan matakai ne domin ragewa mutane radadin zaman gida. Za a ke fita daga karfe 10 na safe zuwa 2 na rana a ranakun Lahadi da Laraba da Juma'a.

Sannan za ayi aiki kai da fata da jami'an tsaro da hukumar Hisba don tabbatar da cewa mutane su bi dokokin tsafta da bai wa juna tazara da wanke hannu.

Ya kuma kara da cewa za suke raba takunkumi ga duk wanda zai shiga masallaci, hakazalika za ake bada sinadarin tsafttace hannu kafin a shiga masallatai.

"An umarci Malaman Masallatan Juma'ah da su tabbatar duk wanda zai shiga masallaci sai ya saka safar fuska wato face mask da kuma wanke hannu da saka sanitizers, sannan a tabbatar an raba sahu kuma an rage huduba tare da rage cinkoso", sanarwar.

Gwamnatin jihar ta bi sahun wasu jihohi ne irinsu Jigawa da Borno da Adamawa da Gombe wajen bari a gudanar da sallolin na Juma'a da na Idi.

Adadin masu cutar korona da aka samu a Kano ya kai 842, inda jihar ke biye wa Jihar Legas wadda ke da kusan kaso ɗaya cikin uku na yawan masu cutar a Najeriya.