Wasu sojojin Najeriya sun yi Allah-wadai da Buratai

BBC
Bayanan hoto,

soji biyu sun rasa rayukansu kuma uku sun jikkata sakamakon taka wani abin fashewa da suka yi

Rundunar sojin Najeriya ta ce za a binciki kwakwalwar sojojinta da suka dauki wani bidiyo inda suke Allah-wadai da shugabancin rundunar da ke jagorantar yakin da suke yi da mayakan Boko Haram.

Wata sanarwa da hedikwatar tsaro ta kasar ta fitar ranar Alhamis, rundunar ta ce an yi wa jami'an rundunarta ta musamman da ake kira KANTANA JIMLAN da ke yanki a Buni Yadi - Buni Gari da ke karamar hukumar Gujba a jihar Yobe kwantan bauna a ranar 18 ga watan Mayu.

Sanarwar ta ce soji biyu sun rasa rayukansu kuma uku sun jikkata sakamakon taka wani abin fashewa da suka yi, an kuma ƙona wata babbar tankar yaki yayin wannan hari.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

soji biyu sun rasa rayukansu kuma uku sun jikkata sakamakon taka wani abin fashewa da suka yi

An kashe mayakan Boko Haram uku wasu dadi masu yawa da ba a tabbatar ba sun tsere da raunika a jikinsu, in ji sanarwar.

Sakamakon rudewa da rikicewar kwakwalwar wasu sojoji biyu da suka tsira daga harin suka dauki bidiyon wanda suke Allah-wadai da rundunar sojin da kuma Hafsan sojin kasa Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai.

A bidiyon, an ji muryar wasu sojoji cikin kuka suna cewa "yadda ake kula da mu bai kamata ba, an sayar mana da 'yancinmu. Burutai, wannan ba alheri ba ne a wajenka, ku duba yadda suka yi mana kofar rago".

Wannan ne karon farko da shalkwatar tsaron kasar ta fito karara ta amince da dakarunta da ke fagen daga sun nuna rashin jin dadi da halin da suke gudanar da aikinsu a ciki.