Coronavirus a Najeriya: Likitoci sun janye daga yajin aiki a Lagos

liktoci

Asalin hoton, Getty Images

Likitoci a jihar Lagos da ke Najeriya sun janye daga yajin aikin da suka tsunduma ranar Laraba saboda zargin da suka yi wa cewa 'yan sanda suna musuguna wa ma'aikatan lafiya a yayin tabbatar da dokar kulle.

Kungiyar likitoci ta kasar reshen jihar Lagos ta ce daga karfe shida na yammacin Alhamis ma'aikatanta za su koma bakin aiki.

A sanarwar da suka fitar, likitotin sun ce sun janye daga yajin aiki ne saboda tabbacin da hukumomi suka ba su cewa ba za su ci gaba da musguna wa ma'aikatan lafiya ba.

Tun da fari, kungiyar likitocin ta ce ma'aikatanta za su yi zamansu a gida har sai 'yan sandan sun daina musguna musu.

Kungiyar ta bayyana cewa musgunawar da ake yi musu 'ta kai mummunan yanayi'.

Ta bayyana cewa sau da dama 'yan sanda suna hana motar daukar marasa lafiya wucewa zuwa inda za ta je, a wasu lokutan ma ana yi wa direbobin da ke ciki barazanar tsare su.

A watan jiya ne Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya sanar da sanya dokar hana fita daga karfe takwas na dare zuwa karfe shida na safe, ko da yake ya ce za a bar ma'aikata na musamman, irin su ma'aikatan lafiya da 'yan jarida da kuma jami'an tsaro, su rika zirga-zirga.

Sai dai duk da wannan sanarwar, kungiyar likitocin ta ce jami'an tsaro ba sa biyayya ga umarnin shugaban kasar.

A sakon da ta fitar ranar Laraba, rundunar 'yan sandan kasar ta yi yunkurin wayar da kan 'yan kasar kan abin da ake nufi da ma'aikata na musamman, tana mai cewa 'ma'aikatan da aikinsu ya zama wajibi, ciki har da ma'aikatan lafiya na cikin wadanda za a bari su rika zirga-zirga'.

Sai dai kungiyar likitocin ta bukaci rundunar 'yan sandan ta ba ta takarda a rubuce wacce za ta nuna cewa da gaske take.

Ta kara da cewa musgunawar da ake yi wa ma'aikatan lafiya ta sanya ba za su iya gudanar da aikinsu yadda ya kamata ba.

Ya zuwa ranar Laraba, mutum 6677 ne suka kamu da cutar korona a Najeriya, yayin da mutum 1840 suka warke, ko da yake cutar ta halaka mutum 200.