Za a buɗe gasar Hikayata ranar 1 ga watan Yuni

Wannan ne karo na biyar da ake gudanar da gasar

Za a buɗe gasar ƙagaggun labaran Hausa ta Hikayata ta BBC Hausa ta wannan shekarar a ranar 1 ga watan Yuni mai zuwa.

Sanarwar da BBC ta fitar ranar Alhamis ta ce za a rufe gasar ranar 24 ga watan Agusta mai zuwa.

Za a bayyana ƙa'idojin gasar a shafin intanet na BBC Hausa - bbchausa.com da zarar an buɗe gasar.

BBC ta ƙirƙiro gasar rubutun gajerun labaran ne a 2016 domin bai wa mata damar bayyana irin hazaƙar da suke da ita.

BBC na maraba da kagaggun labaranku cikin harshen Hausa, wanda bai gaza kalmomi 1000 ba, kuma kar ya wuce kalma 1,500.

Akwai alkalan gasar da za su zaɓi gwarzuwar da labarinta ya fi, da kuma mutum biyu da ke biye mata, da sauran labaran da suka cancanci yabo.

Shugaban Sashen Hausa na BBC Aliyu Tanko ya ce : "Wata dama ta ƙara samuwa ta zaƙulo haziƙar marubuciyar Hausa domin bayyana ƙwarewarta da gogewarta a rubutu da sauran sassan duniya.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"An san mata tun da daɗewa a kasar Hausa wajen bayar da labarai don haka wannan gasar ta basu damar ci gaba da wannan al'ada.

Mun samu gagarumin ƙari na mata da suke karanta labaranmu tun da muka fara wannan gasa shekara biyar da suka gabata."

Shugabar Sassan Yammacin Afirka na BBC, Oluwatoyosi Ogunseye, ta ce: "BBC Hausa tana bayar da labarai na mata babu dare babu rana ta hanyar shirya irin wannan gasa kuma muna farin cikin game da yadda mata suke shiga wannan gasa duk shekara. Mata su ne ƙashin bayan labaran da BBC take bayarwa kuma za mu ci gaba da inganta wannan gasa kowacce shekara."

Safiyya Ahmad, 'yar asalin karamar hukumar Zariya ce,ta zama gwarzuwar gasar Hikayata ta 2019 da labarinta mai suna "Maraici".

Shi dai "Maraici" labarin wata baiwar Allah ce da ta rasa mahaifinta tun tana karama. Hajiya Babba ta goya ta har takai minzalin aure daga nan ta yi mata aure. Wannan aure bai dore ba daga karshe dai mijinta ya sake ta. Ita kuma Hajiya Babba ta yi mata korara rashin mutunci bayan auren ya kare.

Aisha Muhammad Sabitu ce ta soma lashe gasar da labarinta mai suna "Sansanin 'Yan Gudun Hijira".

Labarin nata ya yi tsokaci ne kan mawuyacin halin da 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu suka samu kansu a wani sansani da ke jihar Adamawa.