Kotu ta yanke wa Yunusa Yellow hukuncin daurin shekara 26

Yunusa

Asalin hoton, Yunusa Yellow

Babbar kotun da ke zama a birnin Yenagoa da ke jihar Bayelsa ta yanke wa Yunusa Dahiru da aka fi sani da Yunusa Yellow daurin zaman gidan kaso na shekara 26 bisa samun shi da laifin safara da cin zarafin Ese Oruru.

A shekarar 2015 ne dai mahaifan Ese Oruru suka yi zargin Yunusa Yellow da yin 'garkuwa' da yarsu, ya kuma kai ta jihar Kano inda ya tilasta mata aurensa har ma aka samu juna biyu.

Wannan batun dai ya jawo ka-ce-na-ce tsakanin 'yan kudu da arewacin Najeriya, musamman bayan da ta bayyana cewa Ese Oruru ta musulunta inda ta bar addininta na Kirista.

Ese Oruru dai ta zama Aisha bayan da ta musulunta amma daga baya sai rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta kubutar da Ese Oruru mai shekara 13.

Alkalin kotun dai ya ce ba a samu Yunusa Yellow da laifin na farko ba na garkuwa da mutum, to sai dai ya ce an same shi da laifin safarar kananan yara da yin jima'i ba tare da amincewa ba da cin zarafi.

Mai shari'a Jane Iyang daga karshe ya yanke wa wanda ake tuhumar hukuncin zaman gidan kaso na shekara 26.

To sai dai bisa doka, Yunusa Yellow na da hurumin daukaka kara.