Eid-al-Fitr: Kwamitin ganin wata a Najeriya 'na neman mutanen da suka ce sun ga wata'

Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kwamitin ya ce yana so ya tabbatar da sahihancin abin da suka gani

Kwamitin duba wata na Fadar Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce yana neman agajin mutane da su taimaka masa wurin neman duk wanda ya ce ya ga watan Shawwal a daren Juma'a.

Shugaban kwamitin, Farfesa Usman el-Nafaty ne ya tabbatar wa BBC hakan, inda ya ce suna neman mutanen ne domin tattaunawa da su da nufin tabbatar da sahihancin abin da suka gani.

Tun farko wani shafin Facebook ne mai ɗauke da sunan kwamitin ganin watan ya wallafa sanarwar cewa ana neman mutanen.

"Muna roƙo idan kuna cikin waɗanda suka ga watan Shawwal na shekarar 1441 a kowanne lungu da saƙo na Najeriya ranar Juma'a, ko kuma kun san wanda ya gani, ko kun san yadda za a cimma wanda ya gani to ku bayyana mana a nan," in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa: "Mambobin kwamitin ganin wata na son su tattauna da mutanen game da batun domin su taimaka musu (kwamitin) wurin aiwatar da aikinsu a matsayinsu na masu bai wa Mai Alfarma Sarkin Musulmi shawara."

A daren Juma'a ne dai kwamitin ya bayar da sanarwar cewa ba a samu rahoton ganin wata ba, saboda haka za a cika azumi 30, inda za a yi sallar Idi ranar Lahadi.