Sojoji sun 'kashe 'yan fashi 135' a Katsina da Zamfara

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, Nigerian Army

Bayanan hoto,

Rundunar sojan Najeriya ta ce ta lalata sansanoninsu da dama

Dakarun rundunar Hadarin Daji ta sojojin Najeriya sun yi nasarar kashe 'yan fashi 135 a wani hari ta sama a jihohin Kastina da Zamfara cikin kwana biyu.

A wata sanarwa da jami'in tattara bayanai na hedikwatar tsaro da ke Abuja, Manjo Janar John Enenche, ya fitar ranar Asabar ta ce an kai hare-haren ne a ranakun Laraba 20 ga watan Mayu zuwa Juma'a 22, inda ta lalata sansanoninsu.

Daga cikin sansanonin da aka hara akwai Sansanin Abu Radde na ɗaya da na biyu, da kuma Dunya da ke ƙananan hukumomin Jibya da Ɗan Musa dukansu a Jihar Katsina, a cewar rundunar.

Sauran sun haɗa da Sansanin Hassan Tagwaye da Sansanin Maikomi da ke ƙananan hukumomin Birnin Magaji da kuma Zurmi na Jihar Zamfara.

Wannan nasara da rundunar ta yi ikirari na zuwa ne mako ɗaya bayan umarnin da Shugaba Muhammadu ya bayar na kakkaɓe 'yan fashi daga jihohin na Katsina - jihar da ya fito - da kuma Zamfara.

Kungiya mai bincike kan tashe-tashen hankula a ƙasashen duniya, International Crisis Group, ta ce an kashe mutum fiye da 8,000 a rikicin arewa maso yammacin ƙasar cikin shekara 10.

Kungiyar ta ce rikicin ya raba fiye da dubu ɗari 200 da muhallansu a rikice-rikice da kuma hare-hare a yankin.

A baya-bayan nan rundunar ta sha ikirarin samun nasara a kan 'yan bindiga, sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da take tabbatar da rahotannin.