Taliban ta tsagaita wutar kwana uku don bikin Ƙaramar Sallah

Afghan troops

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An samu ƙaruwar kai hare-hare kan dakarun gwamnati a 'yan makwannin nan

Ƙungiyar Taliban ta ba da sanarwar tsagaita wutar kwana uku da gwamnatin Afghanistan wadda za ta fara aiki daga ranar Ƙaramar Sallah a Lahadin nan.

Matakin na zuwa ne bayan ƙaruwar hare-hare daga ƙungiyar 'yan ta-da-ƙayar-baya masu tsattsauran ra'ayi kan dakarun gwamnati cikin makwannin baya-bayan nan.

Shugaba Ashraf Ghani ya yi maraba da sanarwar, kuma ya ce sojojinsa za su mutunta sharuɗɗan wannan yarjejeniya.

Yarjejeniyar ta tsawon kwana uku mai yiwuwa ne ta haɓɓaka fatan raguwar ayyukan tarzoma na tsawon lokaci a ƙasar.

Sai dai ba a iya tsawaita wata makamanciyar wannan yarjejeniya da aka cimma saboda sallar idi ba a shekara ta 2018.

"Kada ku kai duk wani hari kan abokan gaba a ko'ina. Amma idan maƙiya sun auka muku, to ku kare kanku," Mai magana da yawun Taliban Zabihullah Mujahid ya bayyana ranar Asabar.

Ya ƙara da cewa an ayyana yarjejeniyar ce taƙamaiman don bikin Sallar Idi, wanda ya kawo ƙarshen watan Ramadan mai tsarki.

"Ina maraba da wannan sanarwa," Shugaba Asharaf Ghani ya wallafa a shafinsa na Tiwita jim kaɗan kuma. "Na umarci [dakarun soji] su yi aiki da yarjejeniyar ta kwana uku amma su kare kansu matuƙar an kai musu farmaki."

Al'ummar Afghanistan da masu sanya na ƙasashen duniya sun yi fatan ganin an rage tarzoma tsakanin ɓangarorin biyu sakamakon sanya hannu kan yarjejeniyar janye dakaru da ƙungiyar Taliban ta cimma da Amurka a watan Fabrairu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Jami'ai kaɗan ne a ƙungiyar tsaro ta Nato ke jin cewa tsagwaron ƙarfin soja na iya yin nasara a kan Taliban

Sai dai an gamu da cikas kan batun ci gaba da ƙarin tattaunawa game da musayar fursunoni, yayin aka samu ƙaruwar hare-hare kan dakarun gwamnati cikin 'yan makwannin nan.

Wani hari da aka kai kan wani asbitin haihuwa da ke babban birnin ƙasar, Kabul a farkon wannan wata ya janyo tofin Allah tsine daga ɓangarori da dama.

Yayin da Taliban ta musanta hannu a hari, lamarin ya harzuƙa Shugaba Ghani har ya ba da umarnin ci gaba da kai hare-hare kan ƙungiyar da ma sauran 'yan ta-daƙayar-baya.

Ya zargi masu gwagwarmaya da makamai da bijirewa kiraye-kirayen da aka sha yi don taƙaita ayyukan tarzoma.

A watan jiya, sai da Taliban ta yi watsi da wani kiran gwamnati na a tsagaita wuta a faɗin Afghanistan don martaba watan Ramadan.

Suka ce "babu hankali" cikin lamarin maimakon haka suka ƙara yawan kai hare-hare kan dakarun gwamnati.