Saudi Arabia: Za a buɗe masallatai daga 31 ga Mayu amma ban da na Harami

Saudiyya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Saudiyya ta shiga rana ta biyar da sanya dokar hana fita ta tsawon sa'a 24 domin hana bukukuwan Sallah

Saudiya za ta soma sassauta dokar kulle daga ranar 21 ga watan Yuni sannan ta cire dokar hana fita kwata-kwata a fadin kasar, bayan kusan wata biyu a yaƙin da take yi da annobar korona.

Za a ɗage dokar ne a ko'ina ban da birnin Makkah. Za a buɗe dukanin masallatai da ke wajen Makkah daga ranar 31 ga watan Mayu, a cewar Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida.

Kasar ta shiga rana ta biyar da sanya dokar hana fita ta tsawon sa'a 24 domin hana bukukuwan Sallah.

Sai dai daga ranar Alhamis jama'a za su more zirga-zirga ta sa'a 9 a kullum. sannu a hankali lokutan za su karu zuwa sa'a 14 cikin mako uku masu zuwa.

Da sannu-sannu za a soma buɗe masalattai da shaguna da manyan kantuna.

Sai dai shagunan aski da wuraren wasanni da na motsa jiki da sauran wuraren da bai wa juna tazara zai yi wahala ba za su buɗe ba, har sai nan gaba.

Saudiyya ta tabbatar da samun mutum sama da 75,000 da sukja kamu da cutar korona da kusan 400 da suka rasu sakamakon cutar.