Coronavirus: Yara na kara shiga damuwa saboda kulle makarantu

Wata matashi na kwance kan gado a gida

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Damuwar kaɗaitaka da rashin tabbas na ƙaruwa tsakanin matasa, in ji masana

Emma mai shekara 14 wadda ba sunanta ba ne na gaskiya, na ta fadi tashi na makonni bayan fama da dokar kulle a Burtaniya.

Kasancewa tare da abokanta ya kan rage mata damuwa, amma yanzu tana fama da kadaitaka.

"Ina zaune a dakina ba tare da sanin yaushe zan koma makaranta ba ko in ga abokaina," ta shaida wa kwamishinan yara na Ingila.

"Na matukar gajiya da zama a nan.

Sai dai ba ita kadai ke fuskantar wannan matsalar ba.

Kwararru na ta gargadin cewa raba yaran da sa'anninsu da kuma killace su ta hanyar dokar kulle ka iya haifar musu da damuwar kwakwalwa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yara matasa sun nuna firgici a wani bincike da Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majisar Dinkin Duniya Unicef ya yi

Kamar yadda Asusun Tallafa wa Kananan Yara na Majisar Dinkin Duniya Unicef ya bayyana, a binciken da ya yi a farkon fitowar cutar korona, yara sun nuna damuwa kan killacesu da aka yi daga iyayensu da kuma abokansu, saboda tsoron kamuwa da cutar.

Gaskiya a makon farko abin ya zo da burgewa, saboda babu makaranta. Amma cikin ƙanƙanin lokaci yara kan shiga damuwa," kamar yadda Ursula Grass, wadda ita ce shugabar makarantar Waldhauschulle da ke kudu maso yammacin Jamus, ta shaida wa BBC.

"Sai sun yi fama da wannan matsalar ganin an kilace su a gida."

Nisantar abokai

Unicef ya ce yara miliyan 1.6 ne suke fama da sabon da suka yi na makaranta a ƙasashe 145. Ba kawai koyon da suke a makaranta ba ne wannan cutar ta kawo wa tsaiko.

"Malamai ba kawai lissafi suke koyawa ba, ko kuma yaruka. Suna koya musu yadda za su yi mu'amala ta yau da gobe, yadda ake nuna damuwa ga wasu, har da yadda ake wasa da abokai," in ji Misis Grass.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dokar kulle da kuma rufe makarantu sun yanke abotar da ke tsakanin 'yan makaranta miliyan 1.6

A kasar da aka ci gaba ta fuskar intanet kamar Jamus, Malamai kan wallafa ayyuka a intanet, kuma suna waya da aike sakonni ta email ga ɗalibansu.

"Amma abota tsakanin yaran ta samu tasgaro, a wajen yara da yawa wannan babbar matsala ce," in ji Misis Grass.

"Makarantu na samar da nishadi, da kuma wata dama ga yara inda suke fadin abin da ke damunsu ga manyansu domin ba su shawara kuma wajene da ake abotar kusa da kusa," in ji Toma Madders daraktan kungiyar agaji ta Young Mind.

Yayin da muka fara shiga cikin matsalar, "makarantu na taka rawa sosai domin taimakawa matasa," in ji Madders.

Yara da dama sun komawa ajujuwansu a wasu kasashen da dama, amma Mista Madders ya yi gargadin cewa kamata ya yi a bude makarantun lokacin da aka tabbatar akwai cikakken aminci",

Sabbin dokokin da aka ƙaƙaba

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Akwai tsauraran dokokin tsafta yanzu a ko'ina a makarantu

Ko ta wane hali, makarantu wurare ne na daban in aka kwatanta da inda suke a makonnin da suka gabata.

Dokokin tsafta, kamar su tilastawa yara wanke hannu da kuma dokar yaro daya ne zai shiga banɗaki, sun zama wajibi a kowacce makaranta yanzu.

A Denmark da Jamus, ana raba yara zuwa ƙananan rukuni, ba tare da suna taba junansu ba.

Wannan rukunin da ake raba su na zuwa ne ta fuskoki daban-daban, amma suna cin abincin ranarsu ne kowa shi kadai, kuma ko wanne na tsayawa ne a inda aka ware masa tare da malamin da ke kula da su.

"Abu ne mai wuya, musamman ga yara ƙanana, idan aka ce ba za su taɓa abokansu ba wadanda aka ware su a aji kuma aka hana su taɓa juna a lokacin hutun rabin lokaci," in ji Misis Grass.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Masana sun ce sanya dokar tazara kan kananan yara za ta iya zama mai wahala

An rufe makarantu a Burtaniya akalla zuwa watan Yuni, Amma Megan mai shekaru 14 ta ce tana fargabar da kyar za ta taɓa abokanta.

Ta shaida wa BBC ta gwammace ta ci gaba da haduwa da su a intanet, amma ba za ta iya rungumarsu ba.

Helen Dood, Fafesa ce a Jami'ar Reading da ke Burtaniya kan halayyar yara, ta ce tilasta dokar ba da tazara abu ne da zai wahalar da kananan yara.

"Ta hanya daya da wannan zai yi aiki shi ne a sanya dokoki masu tsauri, wadanda kuma ba su dace ba ga lafiyar kwakwalwar yara," Farfesa Dodd ta shaida wa BBC.

"Yana da kyau yara su rika jin suna da cikakken 'yanci, su ga za su iya yanke hukunci kan abin da suke so."

'Abu ne da zai iya ruɗarsu'

Zeinab Hijazi, wata kwararriya ce kan lafiyar kwakwalwa a Unicef, ta ce bude makaranta abu ne da ke bukatar taka tsantsan.

"Abu ne da zai iya rudar yaran," ta shaida wa BBC.

"Fargabar da yara za su shiga za ta yi yawa. Sai dai kuma ta gaske ce a wannan lokacin."

Misis Hizaji ta ce akwai bukatar malamai su samu kwarewa kan abin da zai iya taimakawa yara lokacin da suke fama da damuwa.

"Malamai sun fi rayuwa da yaran sama da kowa, kuma sun fi kowa gane yaron da ke da wata matsala," ta ce.

A kudu maso yammacin Jamus, 'yan makarantar Misis Grass na da bukata ta musamman, wanda hakan ke nufin yaran na cikin hadarin kamuwa da damuwar kwakwalwa.

Ta fadi abubuwa da dama game da aikinta na rage wannan fargaba.

Bayanan hoto,

Abin da ta fi mayar da hankali a kai shi ne rage fargabar da ke tare da yaran, in ji Misis Grass

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"Muna yin wasu ayyukan nishadi tare da su," Misis Grass ta ce, kamar zuwa daji mu gasa pizza tare da su.

Bayan hukumomin Jamus sun ba da shawarar a rika amfani da takunkumi, Misis Grass ta fara dinka masu nau'uka daban-daban tare da ɗalibanta.

Na'u'uka masu haske sun tabbata cewa suna jan hankali, wanda ta tallata a Facebook abin da ya sa ta samu masu dinkin sa kai tare da rama takunkumin zuwa sauran cibiyoyi na duniya.

Ta hanyar ƙawata takunkumin nasa, ta ce yanzu dalibanta sun koyi hanyoyin kare kai kuma sun daina tsoron sanya wannan takunkumi.

'Magance damuwa'

Misis Grass ta ce, "Akwai bukatar malamai su riƙa karantar yaran da halayyarsu ba kawai su tsaya kan koya musu karatu ba."

Amma a Burtaniya, Megan mai shekara 14 ba ta snaya wannan a matsayin wata matsala ba. Tana jin cewa malaman ba koyarwa suke ba, kawai suna tsara aiki ne".

Matashiyar na jin cewa an bar ta a baya, saboda faman da take da da karatu daga gida.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Dole mu bai wa yara dama su magance damuwarsu, in ji Farfesa Dodd

Farfesa Dodd ta ce makarantu da iyaye za su iya taimakawa yaran wajen saukaka musu fama da wannan kullen maimakon matsa musu zaman gidan.

"Domin bai wa yara damar koyo a wannan shekara, suna da bukatar a basu lokaci domin farfaradowa daga damuwar da suke fama da ita kafin sake dawowa karatu," Farfesa Doddy ta ce.

"Ya kamata wannan sakon ya zama a bude kuma an fahimce shi, domin zai taimakawa karatunsu."

A Vietnam, Unicef ta nemi gwamnatin kasar ta sauya jadawalin makarantun yara, domin su iya samun lokacin maye gurbin watanni hudun da aka rufe makarantu ciki a shekara mai zuwa.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

An sake bude makarantu a Vietnam a watan Mayu bayan shafe kimanin wata hudu

"Babu wani abun mamaki in ka yi la'akari da irin matsin lambar da iyaye a Vietnam ke sanya wa yaransu wajen koyon karatu da ganin sun yi kokari a makaranta," in ji Simone Vis, wani kwararre a bangaren koyarwa.

"Wannan matsin lambar na ko ina, kuma sa'anni kan iya tasiri ga abokansu"

Lokaci ne na mayar da hankali

Gwamnati da Unicef sun kaddamar da wani shiri a farkon watan nan a kafafen sada zumunta da gidajen yada labarai za a fara tattaunawa kan matsalar kwakwlawa.

Yara na ta tura zanen da suka yi, da bidiyo da kuma sauran abubuwan da ke magana kan cutar korona da firgicin da za a fuskanta in an koma rayuwa.

Bayanan hoto,

Takunkumi mai launi daban-daban na jan hankalin yara, in ji Misis Grass

An fadawa malamai su shaida wa yara yanayin ba irin wanda suka saba da shi ba ne, in ji Misis Vis.

Cikin shirin har da yadda za a fadawa iyaye yadda za su sa yaransu su fahimci cutar.

"Yana da kyau iyaye su rika ba da muhimmanci wajen sauraren yaransu domin su samu kwarin gwiwar fada musu damuwarsu," in ji Misis Vis.

”Yaba da mahimmanci mu rika yabawa yaran akai-akai, saboda sun nuna wata jajurcewa da ba kasafai ake yin ta ba."in ji Misis Vis.