'Yan bindiga sun kashe kusan mutum 60 a Sokoto

An kashe mutane a Sokoto

Asalin hoton, ZAMFARA GOVERNMENT

Rahotanni daga jihar Sokoton Najeriya na cewa an kashe mutane kusan mutum 60 a cikin wasu hare-haren da 'yan bindiga suka kai a ranar Laraba, 27 ga watan Mayu, 202 a wasu kauyuka na karamar hukumar Sabon-Birnin-Gobir.

Ganau sun ce maharan sun kwashe sa'o'i suna ta'adi a kauyukkan ba tare da kowa ya tunkare su ba, haka ma an ce wata mata da 'yan bindiga uku sun mutu a cikin wani harin da suka kai a karamar hukumar Gwadabawa.

Wani jami'i da ya je wuraren da lamarin ya faru ya shaida wa BBC cewa, da misalin karfe uku zuwa hudu har zuwa biyar na yammacin ranar Laraba, suka samu labarin cewa ga mutane nan sun taso da babura kusan 100 daga dajin da ke kusa da Issa sun nufi kauyukan.

Ya ce " Koda muka samu labari sai muka je muka sanar da jami'an tsaro ga abin da ke faruwa, haka har wadannan mutane suka isa garin Garki, anan suka fara daga garin Dan adu'a".

Jami'in ya ce " A wannan gari na Dan adu'a munga gawa a kwance har mutum 13, banda wadanda ake nema, a garin Garki kuwa abin da idanuna suka nuna mini har na dauki hoto naga gawa 19".

Ya ce " A garin Kuzari, an kashe mutum 20 har da limamin garin, garin Kafi ma an kashe mutum 6, sai garin Masawa aka harbi mutum 2".

Ganau din ya ce, idan aka hada jimilar mutanen da ya ga gawarsu sun kusa mutum 60, banda wadanda ake nema.

Ya ce " Barayin shanu da mutane ne suka kai wadannan hari, wanda bai jima ba mai girma gwamna jiha ya kai jaje Sabon Birni a makon da ya wuce wato ranar jajiberin sallah domin jajantawa mutanen garin bisa kashe mutum 19 da aka yi".

Ganau din ya ce " Batun jami'an tsaro mun shaida wa 'yan sanda na Sabon Birni ga abin da ke faruwa, nan kuma suka je garin Garki, to amma abin da ke faruwa basu da kayan aikin da zasu fafata da wadannan 'yan bindiga".

Ya ce " Baya ga rashin isassun kayan aiki, sannan su kansu jami'an tsaron basu da yawan da zasu tunkari wadannan 'yan bindiga".

Jihar ta Sokoto na makwabtaka da jihar Zamfara wacce 'yan fashi da barayin shanu suka addaba.