Coronavirus a Kano: Me ya faru adadin masu cutar ya yi ƙasa?

@KNSMOH

Asalin hoton, @KNSMOH

Wasu ƙwararru a fannin lafiya na bayyana fargaba da damuwa kan alƙaluman masu korona da ake fitarwa baya-bayan nan daga Kano, jihar da ta fi fama da annobar a arewacin Najeriya.

Bayanan da hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ke fitarwa kullu yaumin sun nuna matuƙar raguwa a baya-bayan nan na adadin masu cutar a Kano, duk da ƙaruwar da ake samu a sauran sassan ƙasar.

Ƙididdigar ta nuna mutum uku ne suka kamu a ranar Lahadi, bayan samun mutum tara ranar Asabar. Kafin nan, a ranar Juma'a da Alhamis mutum uku-uku aka gano da wannan cuta.

Ga alama tun daga Alhamis 21 ga watan Mayu lokacin da aka samu adadin mutum 28, ba a kuma fitar da alƙaluman masu cutar da suka kai yawan mutum 20 daga Kano ba har yanzu.

Lamarin ya jefa taraddadi a zukatan ƙwararru game da abin da ke faruwa a jihar, wadda ke fama da ƙaruwar mace-macen da har yanzu ba a tabbatar da sanadinsu ba.

Alƙaluman da ma'aikatar lafiya ta jihar ke fitarwa a shafinta na tiwita kullum na cewa jimillar mutanen da aka gano sun kamu da korona a Kano zuwa ranar Lahadi, 954 ne, cikin gwaji 4,735 da aka yi.

Ƙwararru na da ra'ayin cewa kamata ya yi adadin masu cutar ya zarce abin da ake fitarwa a 'yan kwanakin nan. Mai yiwuwa la'akari da yawan al'ummarta da kuma matsayinta na jiha ta biyu da annobar ta fi ƙamari a Najeriya.

Farfesa Sadik Isa ya ce ko kaɗan ba wai rage alƙaluman masu cutar da aka gano ake yi da gangan ba, a'a. Akwai jerin matsaloli tattare da ƙoƙarin gwaje-gwajen samfuran mutane a jihar.

Shugaban na cibiyar bincike kan cutuka masu yaduwa a Jami'ar Bayero Kano ya ƙara da cewa alƙaluman da ake gani na mutanen da suka kai kansu asibiti ne bayan an yi zargin sun yi hulɗa da masu korona.

Ga alama su kuma jama'ar gari ba sa kai kawunansu don a yi musu gwaji a cibiyoyin da aka tanada a Kano, balle a yi batun mazauna yankunan da ke wajen birnin.

Asalin hoton, @KNSMOH

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Gwamnatin Kano cikin sanarwa da kwamishinan yaɗa labaranta, Mohammaed Garba ya fitar kuma aka wallafa a shafukan sada zumunta ranar Lahadi ta ce a cikin makon jiya kawai sun yi gwajin korona 1,018.

Sanarwar ta ce a cikinsu kuma an gano mutum 72 da suka kamu daga ranar 23 zuwa 30 ga watan Mayu.

Shi dai Farfesa Sadik ya ce kamata ya yi gwaje-gwajen da suke yi a Kano ya ruɓanya, abin da suke yi yanzu ta hanyar fita su riƙa nemo mutane don ba da samfuransu.

A cewarsa "Duk masana aikin kimiyya sun tabbatar cewa in ba an yi wannan bincike (ko gwaji) ba, hankula ba za su taɓa kwanciya ba".

Najeriya dai ta ce ta yi ƙoƙarin haɓaka yawan mutanen da ake gwadawa zuwa 1,000 kullum a ƙasar, duk da yake ana zarginta da zama cikin ƙasashen da ba sa yin gwaji yadda ya kamata a Afirka.

A ranar Lahadin nan yawan masu cutar korona a ƙasar ya zarce dubu goma, kuma mutane fiye da 280 aka ba da rahoton sun mutu sanadin wannan annoba.

Farfesa Sadik ya ce akwai dumbin mutane a Kano da ba su ma yarda akwai korona ba. "Zancen su zo, su biyo ka asibiti a ɗauki samfurinsu, a kawo ɗakin gwaji....don tabbatar da sanin akwai cutar ko babu".

Ta wannan hanyar kaɗai, to ba mu kai ga matsayin da ake so ba, in ji shi.

Akwai ɗakunan gwaje-gwaje da aka tanada kuma an zuba kayan aiki, in ji shi. Bayanan hukumar NCDC sun nuna cewa cibiyoyin gwajin samfurin korona guda uku ne a Kano.

Asalin hoton, @KNSMOH

Bayanan hoto,

Baya ga ƙarin cibiyoyin gwaje-gwajen da aka buɗe, gwamnatin jihar ta ce ta samar da cibiyoyin kwantar da masu korona da dama a Kano

Ban da wasu na-tafi-da-gidanka da hukumomin jihar ke cewa sun ƙara tanada don wannan aiki Farfesa Sadik ya nanata buƙatar wayar da kai a tsakanin jama'a game da cutar.

A cewarsa su kansu ma'aikatan lafiya, sai sun sake zage dantse kuma su riƙa fita suna karɓo samfuran jama'a maimakon su zauna jiran mutane.

Haka zalika, ya buƙaci mayar da aikin gwaje-gwajen korona zuwa na kwana, don haɓaka bin sawu da aikin gwajin.