Coronaviirus a Ghana: Za a bude masallatai da coci-coci

Ghana President Nan Addo

Asalin hoton, Getty Images

Shugaba Nana Akufor-Addo na Ghana ya sanar da shirin gwamnatinsa na sassauta hana jama'ar kasar yin tarurruka.

A karkashin sabuwar dokar, za a bude masallatai da coci-cocin kasar - sai dai mutum 100 ne kawai za a bari su halarci wuraren ibadan a lokaci guda.

Ranar Juma'a mai zuwa dokar za ta fara aiki, fiye da wata biyu bayan da gwamnatin kasar ta kafa dokar hana fita a fadin kasar domin dakile yaduwar cutar Covid-19.

Kawo yanzu, Ghana na da fiye da mutum 8,000 da suka kamu da cutar kuma mutum 36 sun rasa rayukansu.

A wani jawabi da ya gabatar ta talabijin, Shugaba Akufor-Addo na Ghana ya ce dalilan gwamnatinsa na sassauta dokar hana jama'a taruwa a wuri guda an gina shi ne bisa wani bincike da ke nuna tasirin abin kan tattalin arzikin kasar da kuma cewa kasar na iya tunkarar duk wata annoba da ka iya barkewa.

A karkashin sabon tsarin da aka fitar, gwamnatin kasar ta kyale Musulmi da Kirista su gudanar da ibadarsu amma kada masu ibadan su zarce mutum 100 a lokaci guda, kuma ka da tsawon ibadar ya zarce sa'a guda.

Tilas kuma a sanya takunkumi da bayar da tazara a masallatai da coci-coci.

Za a kuma bude makarantun kasar, amma 'yan aji na karshe ne kawai za su halarci makarantun.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tun tsakiyar watan Maris ita ma Ghana ta shiga jerin kasashen duniya da suka sanar da dakatar da kwallon kafa saboda korona

An kuma kyale mutane su gudanar da taruruka da bukukuwan aure da wasannin da masu yi ba taba juna, da kuma tarurrukan siyasa - wadanda ba za a bari masu taron su wuce mutum 100 ba.

Amma sabuwar dokar ta tsawaita hanin gudanar da bukukuwan al'adun gargajiya da wasanni kamar na kwallon kafa da halartar wuraren shakatawa kamar kulob-kulob da sila da gangamin siyasa.

Shugaban na Ghana ya ce gwamnati za ta kwaso 'yan kasar da suka makale a kasashen ketare, amma tilas a killace su na mako biyu bayan gwaje-gwajen da za a yi mu su domin tabbatar da ba sa dauke da kwayar cutar korona.

Shugaban ya kuma jaddada cewa iyakokin kasar za su ci gaba da zama a kulle har wani lokaci mai zuwa.