Ɓarayi sun ci amanarmu ba zan sake sulhu ba – Masari

Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari

Asalin hoton, @GovernorMasari

Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya ce ɓarayi masu fashin daji sun ci amanarsu bayan sun yi sulhu da su domin samar da zaman lafiya a yankin arewa maso yammaci.

A hirar da BBC ta yi da gwamnan na Katsina a Instagram, ya ce ƴan ta'addan da ke kai hare-hare akwai har da na Nijar baya ga na jihohin Zamfara da Kaduna da suke makwabtaka da Katsina.

Gwamna Masari ya ce gwamnatinsa ce ta fara ƙirƙiro yin sulhu a 2016, kuma a cewarsa sulhun ya yi tasiri da farko amma kuma daga baya ƴan bindiga suka ci amanar gwamnati.

Ya ce waɗanda ba su yarda da sulhun ba ne suka dawo suna kai hare-hare, kuma yanzu a cewar gwamnan jami'an tsaro ne ya kamata su yi sulhu da ɓarayi.

"Mun bi hanyar sulhu don samun zaman lafiya kuma mun yi iya bakin kokarinmu amma zaman lafiya ya gagara," in ji gwamnan Masari.

Ya ce a sulhun da aka yi da ɓarayin ne ya sa aka soke ƴan sa-kai tare da buɗe masu hanyoyin da za su yi zirga-zirga da shanunsu da kuma hanyar da za su kawo kayansu kasuwa.

Gwamnan na Katsina ya kuma ce Koken da suka yi ne ya sa gwamnatin Tarayya ta turo sojoji da jirage akalla biyar da za su yi aiki tsakanin Katsina da Zamfara har zuwa Sokoto domin kakkabe ɓarayin.

Amma ya ce jami'an tsaron na kukan rashin kayan aiki. "Ba su da wadatattun kayan aiki, suna bukatar kayan aiki sosai," in ji Masari.