Coronavirus a Najeriya: Yawan wadanda suka warke sun kai 3,239

@NCDCGOV

Asalin hoton, @NCDCGOV

Bayanan hoto,

Hukumar NCDC ta ce Najeriya na haɓaka ƙoƙarinta wajen wayar da kai da faɗakar da al'umma a unguwanni da yankuna

Yawan masu cutar korona a Najeriya ya kai wani gagarumin mataki, domin yana gab da kai wa dubu 11.

Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta ƙasar ta nuna cikin alƙaluman da fitar cewa an gano ƙarin mutum 241 ranar Talata da suka sake kamuwa da ƙwayar cutar.

Wannan adadi na ranar Talata ya nuna an samu raguwa idan aka kwatanta da kwanaki biyu jere da aka samu sama da mutum dubu dauke da cutar.

A yau ma Legas, jihar da annobar ta fi tsanani a Najeriya, an sake samun mutum 142 da suka kamu.

Abuja kuma, babban birnin Najeriya, mutum 13 ne aka ba da rahoton cutar ta sake shafa.

Haka zalika, alƙaluman NCDC sun nuna cewa an kara samun wadanda suka rasu sakamakon cutar inda yanzu adadinsu ya kai 314.

Sai dai kuma, an kara samun wadanda suka warke abin da a yanzu adadinsu ya kai 3,239.

Jihar Oyo ita ce tazo ta biyu a yawan wadanda suka kamu da cutar a ranar Talata inda take da mutum 15, sai Kano 12, sai Edo 11, inda aka gano mutum 10 da suka kamu da cutar a Delta.

Kaduna tana da mutum 9, sai Rivers 9, Borno mutum 8, sai Jigawa 4.

A Gombe an sake gano mutum Uku, Plateau mutum 3, Osun 1, sai Bauchi 1.

Asalin hoton, @NCDCgov

Bayanan hoto,

Tun bayan ɓarkewar annobar korona, Najeriya ta yi ƙoƙarin ƙara yawan cibiyoyin gwaje-gwaje da horas da jami'an lafiya

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Muhimman bayanai kan annobar korona

A wani abu da ba a taɓa gani ba tun bayan ɓullar annobar korona a Najeriya, hukumomin ƙasar ranar Asabar 30 ga watan Mayu, sun ba da rahoton gano mutum 553 da cutar ta sake harba.

An fara gano cutar korona a Najeriya ne a jikin wani baturen kasar Italiya ranar 27 ga watan Fabrairu bayan ya shiga kasar ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

Shi da mutum na farko da ya kamu da cutar ranar 20 ga watan Maris a arewacin Najeriya, Mohammed Atiku duk sun warke kuma an sallame su daga asibiti.

A ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu ne cutar korona ta yi sanadin mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya. Shi ne mutum mafi girman mukami da ya mutu dalilin korona a kasar.

Gwamnoni irinsu Bala Mohammed da Nasir El-rufa'i da kuma Seyi Makinde na jihar Oyo duk sun kamu da annobar kafin su warke daga bisani.

Bayan kimanin wata uku da ɓullar cutar a Najeriya, karon farko hukumomi a ranar Laraba 27 ga watan Mayu sun ce mutum biyu sun kamu da korona a jihar Kogi.

Wasu sun yi ta zargin cewa annobar ta daɗe ta shiga jihar, rashin yin gwaji ne ya sa aka shafe tsawon lokaci kafin a iya tabbatar da ita.

Jiha ɗaya ce a hukumance har yanzu ba a samu ɓullar korona cikinta ba a Najeriya. Ko da yake, ita ma wasu na cewa mai yiwuwa ne akwai annobar a jihar ta Cross river, amma gwaji ne zai tabbatar da gaskiya.

Hukumomin Najeriya dai sun ce sun rubanya yawan gwaje-gwajen da suke yi a kasar, inda a yanzu suka ce a kan yi gwaji kimanin dubu guda cikin sa'a 24.

Ga jerin bayanan jihohin da korona ta bulla cikinsu ya zuwa daren Talata 02 ga watan Yuni.

Asalin hoton, NCDC