Kotu ta yi watsi da dakatar da 'yan majalisar dokokin jihar Kano

EFCC ta ce Danja ya sha cirar kudaden lokacin da shi kadai ne zai iya cewa ko an gudanar da ayyuka kafin biyan kudi

Asalin hoton, Kano asssembly

Bayanan hoto,

Mai shari'a Lewis Alagoa ya ce dakatarwa da aka yi wa 'yan majalisar ta saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya

Wata kotun tarayya da ke jihar Kano a arewacin Najeriya, ta yi fatali da dakatarwar da Majalisar dokokin jihar ta yi wa 'ya'yanta biyar bisa zargin keta dokokin majalisar.

A watan Maris ne shugaban majalisar, Abdulazeez Gafasa ya sanar da dakatar da 'yan majalisar ne bayan sun ki amincewa da kudurin cire tsohon Sarkin Kano Muhammad Sanusi na II.

An dakatar da 'yan majalisar ne zuwa wata shida, ko da yake nan-take suka garzaya kotu don kalubalantar dakatarwar.

Da yake yanke hukunci ranar Alhamis, Mai shari'a Lewis Alagoa ya ce dakatarwa da aka y iwa 'yan majalisar ta saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ya umarci majalisar ta mayar da 'yan majalisar bakin aikinsu.

Sai dai wani dan majalisar ya shaida wa BBC cewa za su daukaka kara kan hukuncin kotun.

Waiwaye

Shugaban majalisar, Abdulazeez Gafasa ne ya sanar da dakatar da Garba Ya'u Gwarmai da Labaran Audu Madari da Isyaku Ali Danja da Bello Muhammad da kuma Salisu Ahmad Gwangwazo.

Ya ce sun dauki matakin ne saboda yunkurin da 'yan majalisar suka yi na dauke sandar majalisar.

'Yan majalisar dai sun yi yunkurin dauke sandar ne saboda zargin da suka yi cewa gwamnatin Abdullahi Ganduje ta hada baki da wasu 'yan majalisar domin yin amfani da majalisar wurin sauke Sarki Muhammadu Sanusi na II.