Abin da za ki yi don kare kanki daga namijin da ke son yi miki fyaɗe

Bayanan bidiyo,

Hanyoyin da mace za ta iya kare kanta daga fyade.

A wannan makon an yi ta musayar ra'ayoyi kan lamarin fyaɗe da ke ƙara kamari a Najeriya musamman yadda ake cin zarafin mata da ƙananan yara ta hanyar fyaden.

A karshen makon jiya kuma an kashe wata dalibar jami'a mai shekaru 22 da ake zargin ta rasa ranta sanadin fyade a wata majami'a da ke kusa da jami'ar Benin a jahar Edo.

Sannan a ranar Litinin rundunar ƴan sandan jahar Jigawa da ke arewacin a Najeriya ta tabbatar da kama mutum 11 da ake zarginsu da yi wa wata yarinya mai shekaru 12 fyade.

Washe garin ranar kuma aka sake kashe wata budurwa mai suna Barakat Bello mai shekara 18 bayan an yi mata fyade a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin kasar.

Hakan ne ya sa muka tuntubi wata kwarariyar lafiyar mata musamman wadanda aka yi wa fyade Alheri S Makama don gaya mana matakan da ya kamata mace ta bi don kare kanta a hannun namjin da ke ƙoƙarin yi mata fyaɗe.

Ga dai abubuwan da ta fada:

1. Sanin cewa fyaɗe na iya faruwa

Yana faruwa kuma ba ya zabar wanda zai faru da shi. Domin idan kina da wannan sani, za ki iya tuna yana iya faruwa tun kafin ya faru.

Za ki iya kare kanki. Kamar idan kina wurin liyafa, ya kamata ki lura da abin da za ki ci ya kamata ki lura da abin da za ki ci a wurin liyafar nan ko kuma irin ruwan da za ki sha.

Domin a irin wuraren nan wani na iya sa miki abu a cikin abin da za ki ci ko ki sha. Don hankalinki ya ɗauke ya samu hanyar da zai miki fyaɗe.

2. Shan jinin jiki

Jikinki na iya faɗa miki cewa inda kike dinnan bai kamata kina wurin ba, ko kuma irin mutanen da ke wurin da kike a lokacin bai kamata ki tsaya a wurin ba.

Idan jikinki ya faɗa miki irin wannan sai ki yi maza ki bar wurin. Ba sai kin tsaya kin ɓata lokaci ba. Yana taimaka wa wurin kiyaye wannan ala'mari da ake kira fyade.

3. Sanin irin wuraren da fyaɗe na iya faruwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kwararru sun ce kina iya sa kafa ki doki gabansa, yana iya sa shi ya razana ya rasa mai zai yi don ki samu ki gudu

Kamar wurin da yake shiru, ba shi da kyau ki yi tafiya ke kaɗai a matsayin mace. Ba kyau ki yi yawo ke kadai a wurin da yake da duhu.

Don haka idan kika samu kanki a irin wadannan wurare, ki tabbatar ba ke kadai ba ce. Yana taimakawa wajen tsare mutum daga fyade.

4. Kare kai

Kamar yin amfani da borkono ki watsa wa mutum a ido ba laifi ba ne, ko kuma amfani da faratanki ki yakushe shi a jiki, hakan na nuna cewa kin yi naki ƙoƙarin na tsare kanki.

Ko kuma ki yi amfani da hannu ko kafa ki doki gabansa, yana iya sa shi ya razana ya rasa mai zai yi don ki samu ki gudu.

Ko kuma ki yi amfani da wani abu da kika samu a wurin, kamar itace ki buga masa a kai ko a ido.

Ko kuma idan kina rike da mukulli a lokacin, za ki iya amfani da shi ki buge shi.

Kada ki damu da abin da kika rike, ki dai yi kokari ki yi amfani da wani abu ki buga masa don ki tsare kanki.

Sannan ki tabbatar kin yi hauka-hauka, kina iya yin ihu don ki ja hankalin mutane, don ki samu a zo a taimake ki idan kin ga kamar ya fi karfinki.