Coronavirus ta kashe kasuwar karuwai a faɗin duniya

  • Daga Vivienne Nunis
  • Mai aiko da rahotanni kan kasuwanci, BBC News
Escort Estelle Lucas stands in her bedroom with her eyes cast down

Asalin hoton, Estelle Lucas

Bayanan hoto,

Estelle Lucas ta rasa kusan dukkanin abin da ta mallaka saboda annobar korona

Yayin da dokar kulle ke ci gaba da aiki, kuma aka rufe wuraren shaƙatawa da gidajen rawa, mata masu zaman kansu sun tsinci kansu a wani irin hali.

Kusan duk abin da suka mallaka ya ƙare a lokaci guda saboda annobar korona.

Kuma gudun kada su rasa abin yi, wasu daga cikinsu suna ci gaba da harkokinsu ta intanet, yayin da wasu kuma suke neman tallafi daga gidajen ba da agaji.

Estelle Lucas ta yi aiki a matsayin karuwa tsawon shekara 10 a birnin Melbourne, inda ta riƙa ƙulla alaƙa da manema karuwai.

Sai dai yaɗuwar korona da kuma dokokin ba da tazara sun janyo haramta karuwanci, abin da ya sa ta shiga damuwa ganin ƙoƙarinta zai tashi a banza.

"Za a iya cewa na shafe wata shida ba na aiki kuma mutane da yawa za su manta da ni," in ji ta.

"Ba zai yiwu na kira kwastomomina ba ta waya, mu yi hira. A wannan harkar tamu ba zai yiwu ba. Akwai buƙatar mu haɗu kuma hakan ba mai yiwuwa ba ne a wannan yanayi."

Kafin zuwan annobar, Estelle ta ce tana samun kuɗi sama da abin da aka saba, sannan tana fatan nan gaba kaɗan ta biya kuɗin gidan da take ciki a birnin Melbourne na Ausrtralia.

Kusan duk abin da ta mallaka ya ƙare. Yanzu tana ƙoƙarin ci gaba da harkoki ta intanet amma ta ce hakan ba zai maye gurbin haɗuwa a zahiri ba.

Asalin hoton, Estelle Lucas

Bayanan hoto,

Estelle Lucas ta ƙirƙiri wani zaure a intanet domin tallafa wa sauran abokan sana'arta masu zaman kansu yayin annobar

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"Abin haushin kuma shi ne, akwai abubuwan da ba za ka iya maye gurbinsu ba," ta ce. "Na yi ƙoƙarin komawa intanet amma ba kowa ne ya iya amfani da ita ba.

Wasu daga cikin abokan hulɗata ma ba su san yadda ake amnfani da wayar zamani ba."

Yayin da gwamnatoci ke buɗe harkokin kasuwanci irin su gidajen abinci, babu shirin buɗe harkokin karuwanci.

Waɗannan matakai da kuma rashin tabbacin abin da zai faru nan gaba sun sa karuwai cikin halin damuwa sosai.

"Ina cikin damuwa don ganin ƙoƙarina zai tashi a banza, sai dai kawai na ci gaba da fafutuka kamar sa'ad da na fara wannan sana'a," in ji ta.

Kazalika ta ce tana kula da lafiyar abokan hulɗarta. "Za ma su zo ne? Ana ta yaɗa labaran tsoratarwa a gari."

Wani shirin tallafi na gwamnatin Australia ya fara aiki domin agaza wa 'yan kasuwar da annobar korona ta shafa. Amma kafin mutum ya samu tallafin, sai ya gabatar da shaidarsa ta biyan haraji.

Abin da masu zaman kan nasu da suka hada da 'yan ci-rani ba za su iya gabatarwa ba.

Matsala ce da masu zaman kansu ke fuskanta a kasashe da dama na fadin duniya, cewar Teela Sanders, wata farfesa a Jami'ar Leicester.

Ta ce: "Gwamnati tana kyautatawa sosai wajen samar da tallafi ga mutane da dama, musamman wadanda suke da aikin yi na kashin kansu, amma babu mata masu zaman kansu a cikin tsarin.''

Bayanan bidiyo,

Binciken da BBC ta yi ya gano cewa har yanzu wasu gidajen karuwan suna ci gaba da cin kasuwa

"A wasu kasashen da aka ci gaba, mata masu zaman kansu yawanci su ne wadanda 'ya'yansu da 'yan uwansu suka dogara da su. Don haka wannan ya shafi dukkan zuri'ar,'' in ji Farfwsa Sanders.

Niki Adams mai tattara bayanai kan masu karuwanci ta yarda da wannan batu.

Ta shaida wa BBC cewa yawanci mata masu sana'ar karuwanci uwaye ne a Burtaniya, kuma idan suka ci gaba da yin sana'ar tasu, to lallai suna tsananin bukatar kudi ne.

Amma wasu da dama sun samu kansu a halin da ba za su iya ci gaba ba - ko da kuwa suna son yin hakan.

A gidan karuwai na Daulatdia a Bangladesh, 'yan sanda sun hana shiga, suna hana mutane shiga.

Bayanan hoto,

"Nazma" ta ce ko da an buɗe gidan nasu za ta ji tsoron karɓar mai buƙata don kuwa ba ta sani ba ko yana ɗauke da ƙwayar cutar

Yana daya daga cikin manyan gidajen karuwai na duniya inda mata 1,300 ke zaune da yaransu 400.

Tun a watan Maris aka rufe gidan, inda aka bar mata na fama da sayen kayan bukatun rayuwa tare da dogaro da kungiyoyin agaji don samun tallafi.

''Ba za mu iya sana'armu ba a yanzu, don haka ba mu da kudin kashewa, abin da ban tsoro,'' in ji ''Nazma'', wadda ta faɗa mana wani suna da ba nata na gaskiya ba.

Nazma na tallafa wa yara uku da suke zaune da yayarta can a ƙauyensu.

Ta koma gidan karuwai ne shekara 30 a baya lokacin da take 'yar shekara bakwai da haihuwa. Duk da yake tana buƙatar kuɗi, ta damu game da matsalar da take fuskanta kan sana'arta saboda annoba.

''Ko da za mu iya aiki, rayuwar mutane na cikin hatsarin kamuwa da cutar. Za mu ji tsoron kwanciya da abokan hulɗarmu, don ba mu san waye ya kamu ba,'' kamar yadda ta ce.

Garin Daulatdia yana gaɓar Kogin Padma ne, kusa da wata babbar tashar manyan jiragen ruwa. Ita ce babbar tashar da ta haɗa Dhaka babban birnin Bangladesh da sauran yankunan kudancin kasar.

Bayanan hoto,

Mata 1,300 ne ke rayuwa a gidan karuwan wannan gari, ko da yake yanzu an rufe harkokin nasu

Kafin ɓarkewar annobar, dubban masu manyan motoci na bi ta hanyar kowace rana, suna kai kayan amfanin gona da sauran abubuwa zuwa Dhaka.

Mafi yawan mata da yaran da ke zaune a gidan karuwan safarar su aka yi.

''Da yawan su sato su aka yi tun suna yara aka sayar da su don kawo su nan,'' in ji Srabanti Huda, wata lauya kuma mai kare haƙƙin ɗan'adam a Dhaka.

Yayin da gwamnatin Bangladesh da ƙungiyoyin agaji kan taimaka wa matan da 'yan kuɗin buƙatun rayuwa, Srabantu ta ce ba ya isar su, kuma wasu matan ma ba sa samun komai.

A farkon watan Mayu, Srabanti ta shirya wani aikin ba da tallafi, inda ta rarraba fakitin abubuwan bukatun yau da kullum ga kowacce mace cikin 1,300 da aka yi wa rijista a gidan karuwan.

''Akwai wata mace a gidan da ta ce ta fi wata ɗaya ba ta iya sayen maganinta na ciwon suga ba, yayin da wata kuma ta ce ta fi wata biyu ba ta sayi maganin hawan jininta ba.'' in ji Srabanti.

Bayanan hoto,

Srabanti Huda tana taimaka wa matan da ke gidan karuwan da kayan bukatun rayuwa