Joe Biden: Shin zai iya doke Trump don zama shugaban Amurka?

  • Daga Peter Ball
  • BBC World Service
Joe Biden looks into the distance with US flags behind him.

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Joe Biden na jam'iyyar Dimokrat zai fafata da Shugaba Donald Trump na Republican domin ganin wanda zai shafe karin shekara 4 a fadar White House

Joe Biden shi ne mutum daya tilo da ke tsakanin Donald Trump da kuma karin wasu shekara hudu na tafiyar da mulki a Fadar Wite House.

A hukumance, an tsaida mataimakin tsohon Shugaban Amurka Barack Obama a matsayin dan takarar Jam'iyyar Dimokrat a zaben shugaban kasa da za a gudanar cikin watan Nuwamba.

Ga dumbin magoya bayansa, kwararre ne kan manufofin kasashen waje wanda ya shafe shekaru yana wannan aiki a Washington, kwararre ne wajen iya magana a bainar jama'a sannan rayuwarsa ta kasance cikin tarin kalubale.

A wajen 'yan hamayya kuwa, mutum ne mai yawan subul da baka.

Shin zai iya zama magajin Trump a Fadar White House?

Yana da saurin magana

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Joe Biden ya shiga siyasa kafin a haifi da yawan masu zabe na yanzu

Biden ba sabo ba ne a harkar yakin neman zabe - ya fara aiki a majalisar dattawan Amurka a matsayin sanata a 1973 (shekara 47 da suka gabata) sannan ya gudanar da yakin neman zabensa na farko a 1987 (shekara 33 da suka gabata).

Yana da baiwa wajen jan ra'ayin masu zabe kuma cikin kankanin lokaci ya gamsar da su.

Sakankancewa wajen yi wa taron jama'a jawabi ya kawo karshen kamfen dinsa na farko (wannan shi ne na ukunsa) tun ma kafin a fara shi.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Biden mutum ne mai kwarewa wajen yin magana a bainar jama'a amma yana yawan janyo ce-ce-ku-ce a kafafen yada labarai

A wuraren yakin neman zabe ya yi ikirarin cewa: "Magabatana sun yi aiki a mahakar kwal na arewa maso gabashin Pennsylvania" kuma ya fusata kan yadda suka rasa samun damarmakin da ya kamata a ce sun samu.

Sai dai babu mutum daya cikin magabatansa da suka kasance mahakan kwal - ya ari kalamin ne (da sauran kalaman) da yake furtawa daga wani jawabi na dan siyasar Burtaniya Neil Kinnock, wanda 'yan uwansa suka kasance masu hakon ma'adinai.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Biden ya zama mataimakin Barack Obama daga 2009 to 2017

A matsayinsa na Mataimakin Shugaba Obama a 2009 ya gargadi mutane ta hanyar fadin cewa "akwai yiwuwar mun kuskure da kashi 30%" a kan tattalin arziki.

Sannan watakila ya yi sa'a da aka zabe shi a matsayin wanda zai yi wa shugaban Amurka bakar fata na farko mataimaki bayan da ya bayyana shi a matsayin "bakin Ba'amurke mai kwakwalwa da tsafta."

Duk da wannan furuci, irin goyon bayan da Biden ke samu cikin bakaken fata ya ci gaba da karuwa a yakin neman zaben da ake gudanarwa sai dai a baya-bayan nan cikin wani shiri da mai gabatar da shirin Charlamagne Tha God Biden ya sake furta kalami na ban mamaki: "Idan kana da matsalar gane wanda kake tare da shi tsakanin ni da Trump, toh kai ba bakar fata ba ne." lamarin da ya bar baya da kura.

Asalin hoton, THE BREAKFAST CLUB ON POWER 105.1/Via Reuters

Bayanan hoto,

Biden ya yi subul da baka yayin wata hira cikin wani shiri da Charlamagne Tha God ya gabatar

Furucin ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafen yada labarai abin da ya sa tawagar masu yada labaransa suka fito domin warware tunanin da ake cewa bai dauki kuri'un bakaken fata 'yan Amurka da muhimmanci ba.

Abu ne mai sauki ganin dalilin da wani dan jarida na muhallar NY Magazine ya wallafa a shekarar da ta gabata "sakin layin da Biden ya yi wani abu ne da tawagar yakin neman zabensa suka fi mayar da hankali don gudun kwata haka a gaba,"

Kwararre wajen iya kamfe

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Sabanin wasu 'yan siyasa, Biden ya fi sakewa idan ya hadu da masu jefa kuri'a

Sai dai akwai wani abu game da kwarewar da yake da ita wajen iya magana - cikin 'yan siyasa masu taka-tsantsan wajen furta kalamai, ana yi masa kallon mutum mai fadin ra'ayinsa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Biden ya lashe jihohi bakwai a zaben majalisar dattawa na Amurka

Zarge-zarge

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Biden ya fuskanci zarge-zarge da dama daga mata kan dabi'arsa

Mata takwas sun fito cikin shekarar da ta inda suka zargi Biden da rungumarsu da sumbatarsu ba tare da izininsu ba sannan wata kafar yada labarai a Amurka ta saka wasu hotuna da ke haska mu'amalarsa da mata a wuraren taron jama'a - wanda a wani lokacin ya hada da shakar kamshin gashin kansu.

A martaninsa, Mr Biden ya sha alwashin "sake kula" a mu'amalarsa da mata.

Sai dai kuma, a watan Maris, Tara Reade ta zargi Biden da cin zarafinta shekara 30 da suka gabata a lokacin tana aiki a karkashin ofishinsa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Taken "Believe survivors" ya samu karbuwa a 'yan shekarun nan

Biden ya musanta zargin kuma ofishin yakin neman zabensa ma ya fitar da sanarwar da ke cewa: "Sam wannan abu bai faru ba."

'Yan jam'iyyar Dimokrat wadanda ke kare wanda suke fatan ya zama shugaban kasa za su nuna cewa fiye da mata 12 sun zargi Shugaba Trump a bainar jama'a da ire-iren abubuwan da suka shafi fyade, amma ta ya ya za a iya rage irin wannan lamarin?

Tun bayan da aka bijiro da gangamin nan na #MeToo, 'yan Dimokrat - har da Biden - sun sha cewa ya kamata al'umma su yadda da mata sannan duk wani yunkuri na karyata zarge-zargen da ake masa zai sa da yawan masu rajin kare hakkin mata su ji ba dadi.

Cikin wata hira ta talbijin da aka yi a baya-bayan nan, Reade ta ce: "Mataimakansa sun sha fadin abubuwa marasa dadi a kaina a kafafen sada zumunta.

"Shi a karan kansa bai yi haka ba amma akwai alamun munafurci a wajen ofishinsa na kamfe da ke cewa komai lafiya - komai ba lafiya ba."

Ofishin yakin neman zaben Biden dai ya musanta wannan zargin.

Kaucewa maimaita kura-kurai

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Hillary Clinton ta fi kwarewa amma ta sha kaye a hannun Donald Trump a zaben shugaban kasa a 20016

Duk da a baya ya zame masa matsala, magoya bayan Biden na fatan tsarinsa - na yin nesa da talakawa - zai kare shi daga fadawa tarkon da sauran 'yan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar Dimokrat suka fada.

Yana da kwarewa sosai a Washington - sama da shekara 30 a majalisar dattawa sannan shekara takwas a matsayin mataimakin Shugaba Obama - amma samun irin wannan kwarewa ba ta cika taimakawa ba.

AI Gore (shekara takwas a majalisar wakilai, shekara takwas a majalisar dattawa, shekara takwas a matsayin mataimakin shugaban kasa), John Kerry (shekara 28 a majalisar dattawa) da Hillary Clinton (shekara takwas a matsayin mai dakin shugaban kasa, shekara takwas a majalisar dattawa) duk sun gaza wajen bige 'yan jam'iyyar hamayyar na Republican a zabukan shugaban kasa na baya-bayan nan.

Magoya bayan Biden suna fatan 'kan'kan da kan da yake da shi na nufin ba zai sha irin wannan wahalar ba.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Obama ya jingina kamfe dinsa kan alkawarin samar da sauyi a 2008 amma Biden zai fuskanci kalubale ya yi irin haka

Ba sau daya ba, Amurkawa sun bayyana cewa za su zabi dan takarar da ya yi ikirarin shi ba dan Washington ba ne amma suke son zuwa Fadar White House domin girgiza siyasar wajen.

Sannan wani abu ne mai kamar wuya a wajen Biden bayan ya shafe kusan shekara 50 yana siyasa.

Sannan za a iya amfani da hakan wajen shafa masa kashin kaji.

Tarihi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A shekarar 1987 ne Biden ya fara tsayawa takarar shugaban kasa

A 'yan shekarun da suka gabata, Biden ya zama kusa a mahimman abubuwan da suka faru a shekarun da suka gabata sannan irin matakan ba lalle su dace da yanayin siyasar da ake yanzu ba.

A shekarun 1970, ya goyi bayan masu sukar tsarin jigilar 'yan makaranta a bas domin hade su da makarantun gwamnati. An sha yin amfani da wannan wajen sukarsa yayin kamfe.

'Yan Republicans na son nuna cewa Robert Gates, sakataren tsaron Obama ya ce "ba zai yiwu a ki son Biden ba" amma "ba dai-dai bane kan da yawan manufofin kasashen ketare da tsaron kasa na sama da shekara 40".

Biden ya sa a ransa cewa zai ci gaba da fuskantar irin haka idan tafiya ta yi tafiya a yakin neman zabe,

Ibtila'in da ya shafi iyalinsa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mai dakin Biden ta farko Nelia ta mutu sanadin hadarin mota tare da 'yarsu

Daya daga cikin dalilan da suka sa Biden yake daban kan akasarin 'yan siyasa shi ne wasu daga cikin iyalansa sun mutu.

A lokacin da yake shirye-shiryen karbar rantsuwar kama aiki, jim kadan bayan ya ci zabe a karon farko a majalisar dattawa, mai dakinsa Neilia da 'yarsa Naomi suka mutu sanadiyyar hadarin mota wanda kuma ya yi sanadiyyar raunata 'ya'yansa biyu maza, Beau da Hunter.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Dan Biden Beau ya zama atoni janar a Delaware sannan ya zama soja a Iraki

Daga bisani Beau shi ma ya mutu sanadin ciwon da ya samu a kwakwalwarsa a 2015, yana shekara 46.

Wadannan mace-mace da aka yi wa Biden ya sa shi shiga cikin mutane - abin da ke nuna duk da ikon da yake da shi a siyasance da kuma arziki, shi ma ya fuskanci irin abubuwa marasa dadi da suka samu sauran Amurkawa.

Amma wani bangaren na tarihin iyalinsa ya sha ban-ban, na daya dansa Hunter.

Mulki, cin hanci da karya?

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Hunter Biden ya janyo wa mahaifinsa ce-ce-ku-ce a harkokinsa na siyasa

Hunter ya zama lauya kuma mai jan ra'ayi mutane kafin sirrin rayuwarsa ya bayyana ga jama'a har ya gaza shawo kan komai.

Mai dakinsa ta farko ta bayyana yadda ya je mu'amala da kwayoyi da shan barasa da zuwa wuraren rawa a cikin takardar neman saki kuma an kore shi daga rundunar sojin ruwa bayan an same shi da shan barasa.

Ya tabbatar wa Mujallar New Yorker cewa wani hamshakin dan kasuwa dan kasar China ya taba ba shi lu'u lu'u. wanda daga baya hukumomin Beijing suka yi bincike a kansa saboda zarge-zargen cin hanci.

Irin wannan rayuwar ta Hunter (a shekarar da ta gabata ya auri matarsa ta biyu, mako daya da haduwa da ita) ta janyowa mahaifinsa abin fade.

Amurkawa da dama na iya tausayawa wanda shaye-shaye ya zame masa jiki amma gaskiyar cewa ya rike mukamai masu kyau a lokaci guda yana nuna yadda rayuwa ta banbanta ga mambobin siyasa, kamar iyalan Biden.

Tsigewa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

An tsige Shugaba Trump amma daga baya majalisar dattawa ta wanke shi a binda ya sa ba a cire shi daga ofishinsa ba

Daga cikin irin ayyukan akwai a Ukraine wanda ya sa ake zargin Shugaba Trump da kokarin sa shugaban kasar ta Ukraine bincikar Hunter kan zarge-zargen cin hanci.

Kiran wayar da ya sa aka tsige Trump a baya-bayan nan da kuma yunkurin cire shi daga kujerar mulki - yunkurin da bai tabbata ba kuma wani abu da Biden zai so a ce bai shafe shi ba.

Harkokin waje

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Biden yana da kwarewa sosai a fannin diflomasiyya

Wata takaddama a kasashen waje na da lahani ga Biden, saboda daya daga cikin abubuwan da yake da karfi a kai shi ne kwarewarsa a fannin diflomasiyya.

A baya ya shugabanci kwamitin harkokin waje a majalisar dattawa kuma ya sha fadin cewa "ya gana da duk manyan shugabannin duniya cikin shekara 45".

Yayin da wannan ke kara bai wa masu zabe tabbacin cewa yana da kwarewar zama shugaban kasa, abu ne mawuyaci a iya hasashen yadda harkokinsa zai shafi masu zabe.

Kamar harkokinsa na siyasa, za a iya cewa bai wuce gona da iri ba.

Ya soki yakin Gulf da aka yi a 1991 sannan ya nuna goyon bayan kutsen da aka yi wa Iraki a 2003 amma ya zama mai caccakar Amurka bisa sa bakin da ta yi.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ana ganin matakin Biden na nuna rashin goyon bayan bai wa sojoji dama a yakin Gulf na farko na daya daga cikin dalilan da ya sa ya yanke shawarar kin tsayawa takarar shugaban kasa a 1992

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Kasancewarsa mutum mai yawan taka-tsan-tsan, ya nuna rashin amincewar ga kudirin Obama kan kaddamar da sumamen da dakaru na musamman suka yi wanda ya halaka Osama Bin Laden.

Abin mamaki, shugaban na al-Qaida ba shi da ra'ayin Biden sosai. Takardun da hukumar leken asiri ta CIA ta saki sun nuna Bin Laden ya ba da umarnin a kai wa Obama hari amma ba tsohon mataimakin shugaban kasar ba saboda yana tunanin "Biden bai shiryawa kujerar shugaban kasa ba, lamarin da ya jefa Amurka cikin rikici."

Ra'ayoyin Biden ba su yi dai-dai da na matasa masu fafutuka a jam'iyyar Dimokrat wadanda suka fi son jin ra'ayoyin da ke nuna kyama ga yaki irin na su Bernie Sanders ko Elizabeth Warren.

Amma kuma ya kasance mai kishin Amurkawa da yawa wadanda suka yi murna da yadda kwararrun makisa suka halaka babban kwamandan sojoji na Iran Qasem Soleimani a wani harin jirgi mara matuki da aka kai cikin watan Janairun 2020.

Kuma a watan Nuwamba mutane ba lallai ne su jefa kuri'unsu cikin farin ciki ba, ba su da wani zabi illa zabar shi kawai.

Nasara ko rashin ta

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Nasara ko rashin nasara, wannan na iya zama babi na karshe a siyasar Biden

Kuri'un wakilai sun sanya Biden a gaban Shugaba Trump da maki biyar zuwa 10 a fafatawar neman kujerar shugabanci a White House, amma da sauran tafiya a zaben da za a yi a watan Nuwamba, kuma da alama akwai fafatawa a nan gaba.

Tuni 'yan takara biyu suka fara fafatawa kan goyon bayan masu zanga-zangar yin tur da cin zalin da 'yan sanda suke yi wa bakaken Amurkawa da kuma yadda gwamnati take tafiyar da barkewar cutar korona.

Batun takunkumin fuska ma ya zama wani batu na siyasa inda Biden yake son a rika hasko shi yana sanye da daya yayin da Trump kuwa yake sukar takunkumin fuskar.

Idan Biden ya ci zabe zai zama wani muhimmin tarihi a siyasarsa; idan ya yi rashin nasara, mulki zai ci gaba da zama a hannun wanda yake yi wa kallon "bai cancanci ya zama shugaban kasar Amurka ba" - wanda ba za a iya aminta da shi ba.

A 'yan shekarun da suka gabata, da yake auna ko ya shiga fafatawar neman shugaban kasa a 2016, Biden ya ce: "Zan iya mutuwa cikin farin ciki ko da ba ni ne shugaban kasa ba.

Amma lamarin ba haka yake ba.