Coronavirus: Ku rika sanya takunkumin fuska a bainar jama’a — WHO

A woman wearing a protective face mask and gloves walks through a disinfection cabin at the entrance to a shopping centre in Moscow, Russia. Photo: 5 June 2020

Asalin hoton, Reuters

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta sauya matsayarta kan batun saka takunkumin rufe fuska inda ta ce a halin yanzu, za a iya ci gaba da saka takunkumin a wurare musamman inda ba za a iya bayar da tazara ba, duk a yunƙurin dakile yaduwar cutar korona.

Hukumar ta bayyana cewa sabbin bayanai da aka samu sun nuna cewa takunkumin zai iya hana bazuwar kwayoyin cutar.

Tuni dama wasu ƙasashe suka bayar da shawara wasu kuma suka tilasta saka takunkumin idan aka fito bainar jama'a.

Hukumar Lafiyar a baya dai ta fito ta bayyana cewa babu wata cikakkiyar hujja da ke nuna cewa dole sai masu cikakkiyar lafiya sun saka takunkumin.

Sai dai a ranar Juma'a, darakta janar na hukumar Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa "sakamakon sabbin hujjojin da ke fitowa, Hukumar Lafiya ta Duniya na bayar da shawara ga gwamnatoci da su ƙarfafa gwiwar mutane wajen saka takunkumi a wuraren da ke da akwai cutar da kuma wuraren da ba a iya bayar da tazara kamar motocin haya da shaguna".

Tun a baya, hukumar ta sha bayar da shawara kan cewa marasa lafiya su rinƙa saka takunkumi.

A halin yanzu, mutum miliyan 6.7 sun kamu da cutar korona inda kusan mutum 400,000 suka mutu tun bayan ɓarkewar cutar.

Me ke ƙunshe cikin shawarwarin da WHO ta bayar?

Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana cewa bincike daban-daban da aka gudanar a makonnin da suka gabata ya jawo ta sauya matsayarta.

Ɗaya daga cikin jagororin ƙwararru a WHO da ke aiki kan Covid-19, Dakta Maria Kerkhove ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa shawarar da WHO ta bayar shi ne a saka takunkumi wanda aka yi da ƙyalle.

Ta bayyana cewa ya kamata takunkumin ya ƙunshi shimfiɗa hawa uku na ƙyallen domin bayar da kariya.

Sai dai waɗanda suka manyanta masu shekaru 60 zuwa sama ya kamata su rinƙa saka takunkumi irin na asibiti musamman a wuraren da ke da akwai ɓullar cutar.

Hukumar ta bayyana cewa takunkumin hanya ɗaya ce kawai ta kare kai daga kamuwa daga cutar - don haka kada mutane su ɗauka cewa saka shi kawai zai kare su daga kamuwa da cutar.