Buhari ya yi kira ga 'yan fashin daji su mika wuya

Shugaban Najeriya muhammadu Buhari

Asalin hoton, Buhari Sallau

Bayanan hoto,

Buhari ya jajantawa mutanen Katsina

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jajantawa al'ummar jiharsa ta Katsina kan hasarar rayukan da aka samu sakamakon hare-haren 'yan bindiga.

A makon da ya gabata 'yan bindiga suka kashe mutane da dama a Katsina cikinsu har da hakimin Yantumaki Alhaji Atiku Maidabino, da shugaban Jam'iyyar APC na karamar hukumar Batsari Alhaji Abdulhamid Sani Duburawa.

Sanarwar da Malam Garba Shehu ya fitar mai taimakawa shugaban kan harakokin watsa labarai a ranar Asabar ta ce, shugaban ya gana da gwamna Aminu Bello Masari a ranar Alhamis kan matsalar tsaro da ta addabi yankin arewa maso yammaci.

Kuma shugaban ya kara bai wa gwamnan da al'ummar jihar Katsina tabbaci kan sabon kokarin da ake na inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma a jihar da sauran sassan kasar.

Sanarwar ta ce yayin ganawar, Buhari ya yi kira ga 'yan fashin daji su fito su yi saranda su mika makamansu ko kuma su kuka da kansu.

"Ba za a yafe wa 'yan fashin da suka kashe wadanda ba su ji ba su gani ba a jihar da duk fadin kasar nan ba," in ji shi.

Shugaban ya kuma ce za a kara kaddamar da farmaki kan masu fashin daji a jihohin Zamfara da Sokoto da Neja da Katsina da Kaduna.

A makon da ya gabata ne gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya shaida wa BBC cewa ba zai sake yin sulhu da 'yan fashi ba saboda sun ci amanar gwamnati.

An dade jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna na fama da hare-haren 'yan fashin daji masu satar shanu da garkuwa da mutane domin kudin fansa, kafin su tsallaka zuwa Sokoto da Neja.