George Floyd: Dubban Amurkawa na zanga-zanga a Washington DC

Protesters march past the Lincoln Memorial in Washington DC (6 June 2020)

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Masu zanga-zanga a Washington DC na cewa ba za su daina fita ba har sai an sauya abubuwa

Dubban Amurkawa na zanga-zanga a birnin Washington DC domin nuna bacin ransu da yadda 'yan sandan kasar ke muzgunawa bakaken fatar kasar, kwana 12 bayan kisan George Floyd da wasu 'yan sanda suka yi a Minneapolis.

Amurkawan sun taru a kusa da ginin majalisar kasar wato Capitol Building da na Lincoln Memorial da kuma wurin shakatawa na Lafayette Park, amma jami'an tsaro sun hana kowa isa Fadar White House.

A can jihar North Carolina kuwa mutane na can suna nuna girmamawa ga gawar Mista Floyd gabanin a binne shi a garin da aka haife shi.

An kuma gudanar da irin wannan zanga-zangar a wasu kasashen duniya masu yawa.

A Birtaniya, dubban jama'a sun hallara a dandalin Parliament Square na birnin Landan domin nuna goyon bayansu ga masu zanga-zangar nuna rashin amincewarsu da yadda ake cin mutuncin bakaken fata duk da cewa gwamnatin kasar ta hana tarurruka saboda annobar korona.

A kasar Austreliya ma, dubban mutane sun yi zanga-zanga a biranen Sydney da Melbourne da Brisbane wanda ya karkata kan yadda ba a mutunta al'ummar Aborigines wato 'yan kasar na asali.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An sauya sunan wani wuri da ke kusa da Fadar White House zuwa Black Lives Matter Plaza

A birnin Washington DC, Magajiyar Garin birnin Muriel Bowser ta yi maraba da dubban mutanen da suka hallara a wani layi da ke kusa da Fadar White House, layin da ta sauya wa suna zuwa Black Lives Matter Plaza.

Ms Bowser ta ce jama'an da suka taru a wurin sun aika wa Mista Trump wani muhimmin sako.

Ta ce: "Bai dace a rika amfani da sojojin kasarmu haka ba, bai kamata a umarce su da su far wa Amurkawa ba. A yau mun ce 'bamu yarda ba': a Nuwamba kuma za mu ce 'na gaba'."

Ms Bowser ta nemi Mista Trump ya janye dukkan sojoji da jami'an tsaro na gwamnatin tarayya daga cikin babban birnin na Amurka, domin ta ce "babu dalilin kasancewarsu a birnin".