Coronavirus a Najeriya: Kwana 100 da ɓullar cutar

@JIDESANWOOLU

Asalin hoton, @JIDESANWOOLU

Kwana 100 da ɓullar cutar korona Najeriya, annobar wadda aka fara gano ta ranar 27 ga watan Fabrairu, a jikin wani baturen ƙasar Italiya, zuwa yanzu ta harbi mutane kimanin 12,233 a ƙasar.

Alƙaluman da hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa ta fitar a daren Asabar sun nuna cewa a cikin kwana 100, korona ta kashe mutum 342 a Najeriya.

Haka zalika annobar ta ɓulla a kusan dukkan jihohin ƙasar, in ban da Cross river, ciki har da babban birnin Najeriya, Abuja.

Yawan alƙaluman masu cutar da hukumar NCDC ke fitarwa a kullum ya ƙaru, mai yiwuwa saboda haɓaka gwaje-gwajen da hukumomin ƙasar suka yi.

Alƙaluma na baya-bayan nan da hukumar ke fitarwa na zuwa ne cikin adadin ɗaruruwa maimakon gommai kamar a makwannin farko-farko.

Ko a ranar Asabar 30 ga watan Mayu, hukumar ta ba da rahoton gano mutum 553 da cutar ta sake harba cikin sa'a 24, ba a dai taɓa samun adadi mai yawan haka ba cikin kwana guda a ƙasar.

Haka zalika, kusan rabin mutanen da aka gano sun kamu na cikin jihar Legas, inda cutar ta fara ɓulla. Yanzu dai alƙluman hukuma sun ce akwai masu korona 5,729 a jihar.

Daga ita sai jihar Kano, wadda cutar ta fara bayyana cikinta ranar Asabar 11 ga watan Afrilu. Yawan masu korona a Kano zuwa yanzu ya kusa mutum 1,000.

Asalin hoton, @JIDESANWOOLU

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A baya-bayan nan ƙwararru sun bayyana damuwa kan ƙarancin gwajin da ake samu a Kano, suna cewa cutar na daɗa fantsama cikin jama'a kuma ta hanyar gwaji da killace masu cutar ne kawai za a iya shawo kanta.

Gwamnatin Kano dai ta ce za ta ƙara ƙaimi ta hanyar bin gida-gida wajen gudanar da aikin gwaji a jihar.

Ranar 23 ga watan Maris ne kusan wata ɗaya da fara ɓullar cutar a Legas, aka ba da rahoton samun mutum na farko da ya fara kamuwa da korona a Abuja.

Alƙaluman baya-bayan nan na ƙaruwar masu cutar da ake ci gaba da ganowa a birnin su sa yawan masu cutar ya yi tashin gwauron zabbi zuwa 912.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar ne ya fara sanarwa ta hanyar wani saƙon tiwita cewa ɗansa, Mohammed Atiku ya kamu da korona har ma an kwantar da shi a asibitin Gwagwalada.

Ko da yake a cikin wani saƙon bidiyo da ya taɓa fitarwa daga inda ya yi jinya, Mohammed Atiku ya ce tun ranar Juma'a 20 ga wata, aka tabbatar masa cewa cutar ta harbe shi.

Mohammed Atiku dai na daga cikin mutanen da suka fi daɗewa suna jinyar korona a cibiyar killacewa, kafin sallamo shi bayan ya shafe kimanin kwana 40.

Shi da fitattun mutane kamar Gwamna Nasir elrufa'i na Kaduna da takwaransa na Bauchi, Bala Mohammed da Seyi Makinde na Oyo duk sun yi fama da cutar a tsawon wannan lokaci kuma sun warke.

Haka zalika a tsawon wannan lokaci an samu jihohi irinsu Zamfara da Kebbi, waɗanda suka ce sun sallami duk masu cutar da aka kwantar a cibiyoyin killacewarsu bayan an tabbatar sun warke.

Asalin hoton, Getty Images

Sai dai, bayan kimanin mako guda, kuma an sake samun masu cutar biyu a jihar Kebbi da kuma mutum 12 a jihar Sokoto, kwanaki bayan sallamar duk waɗanda suka kamu.

Jiha ta baya-baya da cutar ta ɓulla cikinta ita ce Kogi, Bayan kimanin wata uku da fara gano cutar a Najeriya, a ranar Laraba 27 ga watan Mayu NCDC ta ce mutum biyu sun kamu da cutar a Kogi.

Wasu sun yi ta zargin cewa annobar ta daɗe da shiga jihar, rashin yin gwaji ne ya sa aka shafe tsawon lokaci kafin a iya tabbatar da ita. Yayin da gwamnatin jihar ke cewa tasirin matakan da suka ɗauuka ne.

Tun ranar Litinin 23 ga watan Maris ne kuma Hukumar daƙile cutuka masu yaduwa ta sanar da samun mutum na farko da ya rasu saboda cutar korona a Najeriya.

Hukumar NCDC ta ce mutumin ɗan shekara 67 ya dawo Najeriya ne bayan ya je ganin likita Burtaniya, a cewarta mamacin (Injinya Sulaiman A-ci-mugu) ya yi fama da wadansu kwantattun cutuka kafin rasuwarsa.

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto,

Engineer Sulaiman ya yi fama da cutar daji da ciwon suga kafin cutar korona ta kama shi

A ranar 7 ga watan Afrilu kuma, Gwamna Masari na jihar Katsina ya sanar cewa Allah Ya yi wa mutum na farko da ya kamu da coronavirus a jiharsa, Dr Aliyu Yakubu rasuwa.

Ya ce likitan wanda ke garin Daura, an ba da rahoton ya yi tafiya zuwa Lagos, kuma bai dade da komawa gida ba, ya kamu da rashin lafiya inda ya kai kansa asibiti kafin cikawarsa.

Cutar korona ta yi sanadin mutuwar Mallam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu

Abba Kyari ya rasu ne a Legas, inda ya koma jinya bayan ya kamu da cutar ranar 24 ga watan Maris..

Bayanan hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa na cewa jihar Legas ce ta fi yawan masu korona da suka mutu zuwa yanzu da mutum 67.

Daga ita sai jihar Kano, inda Allah Ya yi wa mutum 48 rasuwa sanadin cutar. Jihar Borno, mutum 26 ne suka mutu, in ji alƙaluman NCDC.

A Abuja, mutum 22 ne suka rasu sakamakon cutar zuwa yanzu. Yayin da Katsina kuma aka samu mutuwar masu cutar 20.

Ranar 30 ga watan Maris ne kuma shugaban ƙasar ya fara ɗaukar matakin kulle Najeriya, da nufin shawo kan annobar ta korona.

Har yanzu Najeriya ba ta kai ga buɗe harkokin sufurin jiragen samanta ba, haka kuma matakin hana zirga-zirga tsakanin jihohi na ci gaba da aiki.

Duk da yake, an buɗe wuraren ibada a jihohi da dama da kuma babban birnin ƙasar Abuja, amma har yanzu kasuwanni na ci ne rabi-da-rabi.

Kuma ma, gwamnatin ƙasar ta ce ba ta sa ranar komawa ci gaba da harkokin koyo da koyarwa a makarantun Najeriya ba.

Haka zalika, daidai lokacin da ake samun yawan masu cutar, su ma masu warkewa daga korona har a sallame su daga cibiyar killacewa suna ƙaruwa.

Zuwa yanzu, akwai kusan mutum 4,000 da suka warke sarai kuma aka sallamo su har suka koma cikin dangi da iyalansu don ci gaba da rayuwa.