Edward Colston: Yadda aka karya gunkin mutumin da ya yi cinikin bayi

Bayanan bidiyo,

Zanga-zangar yadda aka tumbuke gunkin mai cinikin bayi a Bristol

Masu zanga-zanga a birnin Bristol na Burtaniya sun karya gunkin wani Bature da ya yi fice a cinikin bayi tsakanin Afrika zuwa Turai daruruwan shekaru da suka gabata.

An kafa gunkin Edward Colston ne a wani dandalin a birnin don tunawa da irin taimakon da ya dinga bai wa kungiyoyin agaji da dukiyarsa a zamaninsa.

Sai dai masu zanga-zangar wadanda akwai bakaken fata da dama a cikinsu, sun yi hakan ne don a ganinsu ci gaba da barin gunkin nasa tamkar tunzura mutane ne musamman bakake da hakan ke tuna musu zamanin bauta da kakanninsu suka kasance a ciki.

Msu zanga-zangar sun yi ta ne don nuna adawa da kisan wani bakar fata dan Amurka George Floyd da wani dan sanda ya yi a makon da ya gabata, inda aka yi irin ta a kasashen duniya daban-daban.

Magajin garin Bristol Marvin Rees ya bayyana karya gunkin a matsayin tsokana.

Amma ya ce bai ji wata asara ba bayan da masu zanga-zanga suka tumbuke gunkin tagulla na Edward Colston a ranar Lahadi.

Amma Firaminista Boris Johnson ya bayyana hakan a matsayin "babban laifi."

'Yan sandan yankin sun ce ba a dauki mataki don shiga cikin lamarin ba.

Mai magana da yawun Mr Johnson ya ce: "A ganin Firaminista kan lamarin kasar nan shi ne, inda kowa ke da damar bayyana ra'ayinsa, akwai hanyar dimokradiyya da ya kamata a bi.

"Mutane na iya fafutukar kawar da wani gunki amma abin da ya faru jiya babban laifi ne, kuma a yayin da aka karya dokar wani laifi da ba a yarda da shi ba, dole 'yan sanda za su so su kama masu laifin.

"Firaminista ya san yadda kuke ji, amma a kasar nan muna iya warware matsalolin da ke tsakaninmu a siyasance, kuma idan mutane suna son tumbuke wani gunki to akwai hanyoyin da za su bi a siyasance."

Bayanan hoto,

Marvin Rees ya ce za a dauko gunkin a mayar da shi gidan adana kayan tarihi

Dubban mutane ne suka halarci zanga-zangar lumana da aka yi a birane da dama a fadin Burtaniya a karshen makon nan, da suka hada da Manchester da Wolverhampton da Nottingham da Glasgow kuma Edinburgh.

Amma tashin hankalin da aka samu a Landan a ranar Lahadi ya jawo an yi wa 'yan sanda takwas rauni tare da kama mutum 12.

Gunkin fitaccen mai cikinin bayin na ƙarni 17 ya ɗaɗe yana jawo ce-ce ku-ce a Bristol tsawon shekaru.

Mutum 10,000 ne suka fita don yin zanga-zanga a ranar Lahadi, inda aka tumɓuke gunkin Colston aka kuma jefar da shi a ƙasa, sannan aka jefa shi cikin ruwa.

Mr Rees ya ce za a ciro gunkin daga ruwan nan gaba kuma watakila za a mayar da shi gidan adana kayan tarihi na birnin.

Mr Rees ya ce: "Ina ga mutane suna jin cewa ya kamata su kawar da gunkin ne."

"Ba zan iya runtse ido na zauna da gunkin wanda ya yi cinikin bayi a garin da aka haife ni ba, don hakan tamkar tunzura ni ake yi.''

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto,

An jefa gunkin Edward Colston a cikin ruwa bayan tumbuke shi

Ina ne Bristol?

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Bristol wani birni ne a Burtaniya da ke kusa da gabar Kogin River Avon a kudu maso yammacin Ingila.

Birnin ya zama wata cibiya ta cinikin bayi shekaru aru-aru da suka gabata, tsakanin Burtaniya da Yammacin Afrika da yankin Karebiya.

Tun a karni na 11 aka fara cinikin bayi a Bristol inda aka dinga sayar da bayi Turawa da 'yan kasar Ireland a bakin gabatar tekun garin har zuwa shekara ta 1100.

Bristol ta fara shiga cikin lamarin cinikin bayi tsakanin Afrika da Turai a shekarar 1698 a lokacin da ikon da wani kamfani mai cibiya a Landan na Royal African ya kawo karshe a kan lamarin.

Daya daga cikin mambobin Kamfanin Royal African wani mashahurin dan kasuwa ne Edward Colston, wanda kuma saboda irin taimakon da ya dinga yi wa kungiyoyin agaji da arzikinsa ya sa aka kafa mutum-mutuminsa a birnin don girmamawa da kuma tunawa da shi.

A lokacin da Colston ke aiki da Kamfanin Royal Africa, an kai kusan mutum 80,000 Amurka daga Afrika da suka haɗa da maza da mata da yara a matsayin bayi.

A lokacin mutuwarsa a shekarar 1721, ya sadaukar da dukiyarsa ga ƙungiyoyin agaji kuma har yanzu ana iya ganin ayyukan taimakonsa a kan titunan Bristol da gine-gine.

Har sai lokacin da masu zanga-zanga suka yi fushi a makon nan suka tumbuke gunkin nasa, wanda suke kallo a matsayin wata alama ta cin zarafin bakar fata.

Bayan da aka kawar da gunkin, an dauki hoton wani mai zanga-zanga inda ya dora gwiwarsa a kan wuyan gunkin - yana nuna irin yanayin da ɗan sandan da ya yi sanadin mutuwar George Floyd ya yi masa.

'Yan sanda na ci gaba da bincike

'Yan sanda sun ce jami'ai ''sun dauki mataki'' a wajen don shiga tsakani a yayin da mutane ke tumɓuke gunkin.

Sufuritanda Andy Bennett ya ce ya ji takaici kuma bai gane ba, saboda yadda gunkin ya jawo fushi sosai daga baƙaƙen fata da ke zaune a birnin.

Ya ce 'yan sanda sun gano mutum 17 kan lalata gunkin Colston kuma ana ci gaba da bincike.

Mr Rees ya bayyana zanga-zangar a matsayin wacce 'yan sanda suka shawo kanta.

''Dumbin mutane ne suka yi zanga-zangar amma kaɗan aka kama. Gunkin kawai aka lalata amma mutane ba su fasa kantuna ko lalata wasu abubuwa daban ba,'' in ji shi.

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto,

Mutum dubu 10 ne suka yi zanga-zanga a Bristol

Tuni aka gabatar da wani korafi a intanet inda ake so a maye gurbin gunkin nasa da na Dr Paul Stephenson, wani mai fafutukar na farar hula.

Asalin hoton, Bristol City Council

Bayanan hoto,

An baza takardu a filin wajen da aka cire gunkin

Mr Johnson ya sha alwashin cewa za a kama masu hannu a zanga-zangar adawa da wariyar launin, yana mai cewa ana amfani da damar yin macin ana sace-sace.

Shugaban Jam'iyyar Labour Sir Keir Starmer ya ce tumɓuke gunkin bai kamata ba amma dama ya kamata a ce an daɗe da cire shi.

''Bai kamata a ce a ƙarni 21 kuma a Burtaniya amma muna da gunki a matsayin wata alama da ka kafa ba. Amma dai da kamata ya yi a sauke gunkin cikin nutsuwa da izinin a kai shi gidan adana kayan tarihi a ajiye.''

George Floyd - Abin da muka sani

  • A ranar 25 ga Mayu George Floyd baƙin fata ya mutu ana tsare da shi
  • Bidiyo da ya bazu a kafofin sadarwa an ga ɗan sanda farar fata yana danna guiwarsa a wuyan Mista Floyd kusan minti tara kafin ya mutu.
  • Jami'an ƴan sanda hudu ake zargi wadanda suka kama George Floyd kan zargin kuɗin jabu dala 20
  • Daga cikin jami'an ƴan sandan biyu daga cikinsu Derek Chauvin da Thomas Lane sabbin shiga ne lokacin da al'amarin ya faru.
  • An kori ƴan sandan hudu tare da tuhumarsu kan kisan George Floyd, wanda mutuwarsa ta haifar da zanga-zanga a duniya.