Whatsapp: Me ya sa iyaye a Najeriya ke yawan yada labaran bogi?

A composite image of woman looking at a phone with a WhatsApp logo on a phone

Asalin hoton, Getty Images

Cikin jerin wasikun da muke samu daga marubutan Afrika, 'yar Najeriyar da ta lashe kyautar ƙagaggun labarai Adaobi Tricia Nwaubani ta ce yanzu 'ya'ya na sa idanu kan iyayensu a manhajar Whatsapp.

'Yan shekarun da suka wuce, masu wasannin barkwanci na kwashe tsawon lokaci suna tsokana kan wata mahaifiya a Najeriya da kuma halayyarta ga wayar salula.

Iyaye a kasar suna bukatar yaransu a kusa da su don taimaka musu wajen aika sako da kuma duba musu imel.

Ga kuma yadda kullum suke ba da uzuri game da rashin daukar kiran waya, suna cewa "Wayata na cikin jaka".

Yanzu kuwa, an kara fadada barkwancin kan iyaye mata a ƙasar da kuma halayyarsu game da WhatsApp, manhajar da tafi kowacce shahara a Afrika.

Masu barkwanci a Najeriya kamar Maraji sun ta yin barkwanci musamman kan iyaye mata.

"Kullum da safe mahaifiyata tana amfani da manhajar WhatsApp," a cewar wata mai shekara 39 da ake kira Udo, mazauniyar Legas.

"Lokacin da take cin da take karya kumallo ba ta komai sai duba hotunan da bidiyo a WhatsaApp."

'Sakonni masu ma'ana'

Ba kamar Twitter da Instagram ba, WhatsaApp yana yi ko da intanet ba ta da karfi, kamar dai yadda yake a sauran sassan Najeriya.

Ba ya bukatar lambar sirri ko kuma bayanin mai manhajar, to wadanda suka rayu a baya gabanin samuwar intanet sosai a Najeriya yanzu duk suna iya aiki da shi. A takaice, shi ne abin da suke kashe lokacinsu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wayoyin da ke da intanet da ake iya WhatsApp da su, sun zama ruwan dare a ko ina a Najeriya

Korafin da matasa suka fi yi a Najeriya shi ne adadin sakonnin da iyayensu mata ke aika musu kullum.

"Kana tashi da safe za ka ga sakon bidiyo sama da 10 daga mahaifiyarka", in ji Ihuoma mai shekara 41 da ke zaune a Abuja a Najeriya.

"Kuma ko wanne sako yana farawa ne da 'Dole ka kalli wannan', 'Wannan zai iya taimakon mutum!' wadannan su ne yawancin kalmomin da ake bude sakon da su."

Patty ta ce duk sakonnin da mahaifiyarta mai shekara 76 ke aika mata, sakonni ne masu ma'ana.

Getty Images
My mother was always forwarding different health suggestions... When I pointed out to her that some of them are questionable, she replied: 'You never know, just try it and see.'"
Udo
Resident of Lagos

"Ba na aika sakonni masu wani muhimmanci," in ji ta.

"Dalilin da ya sa nake aika wa yarana saknonin shi ne, su kansu wani bangare ne na samun ilimi, da kuma kara musu kwarin gwiwa, da kwarewar rayuwa. Kuma ina daukarsa a matsayin bibiya da kuma tura bayanai zuwa ga 'ya'yana."

Ihuoma ta rufe irin sakonnin da mahaifiyarta take aika mata a WhatsApp kuma ba kasafai take bude duk wani sakon da ta aiko ba.

A wajen iyayen mata da yawa a Najeriya, damar tura sakonnin da aka rubuta ta WhatsaApp wani abun birgewa ne na musamman.

Yana taimaka musu wajen aika sakonnin addu'a da shawara da kuma bayyana ra'ayoyinsu.

Wata mata da ta yi korafi a Twitter kan mahaifiyarta da ke ajiye albasa a kowacce kusurwa ta dakunan gidanta - da aka ce tana maganin cutuka da dama - ta kuma samu amsoshi daga kawayenta cewa su ma iyayensu mata suna amfani da wannan gurguwar shawarar.

"A dandalin WhatsApp din da danginmu suka bude, kullum mahaifiyata sai ta aiko mana da sakonnin kiwon lafiya, cewa 'idan ka hada wannan da wancan sai kasha," in ji Udo

"Lokacin da na nuna mata shakku kan wasu abubuwan da take aiko wa sai ta ce 'ke dai baki sani ba ki gwada kawai ki gani.'

Mahaifiyarta ta aika mata wani bidiyo yadda aka sace wata da kuma yadda aka kitsa laifin, tana jaddada cewa akwai bukatar yaranta su kalle shi domin su kiyaye kansu.

"Amma ina cire kaina daga dandalin WhatsApp din iyalinmu sai na daina ganin wannan sakon da take aikowa," in ji Udo.

"Dan uwana ya toshe sakonninta, kuma hakan ya yi matukar bata mata rai. Amma babu ruwanta. Kullum sai ta tura masa sakonnin."

Dan kamfai, ciwon daji da kuma wasu sauran gargadi

Mutane da yawa sun shaida mani cewa sun toshe sakonnin iyayensu mata a WhatsApp amma ba sa so su sani.

"Ni ma na taba samun kaina cikin wata tattaunawar intanet game da hakan," in ji Ihuoma.

"Wasu na da ra'ayin toshe sakonnin iyayensu mata amma ba sa iyawa, saboda girman wadanda suka dauke su a iyaye har suka haife su.

Adaobi Tricia Nwaubani
Adaobi Tricia Nwaubani
Affordable internet access became common in Nigeria just a few years ago, so this generation of elderly Nigerians was hardly exposed to the wonders of Photoshop"
Adaobi Tricia Nwaubani
Journalist

Suna kokarin ba su shawara mafi yawan lokuta game da ra'ayin rikau ko kuma iyaye matana da ke da rikon addini wadanda suke da matsala da tsarin rayuwar yaransu.

Misali, wani likita da ba a bayyana sunansa ba ya yi bayanin kan yadda sanya dan kamfai ke janyo cutar daji, yadda matsatstsan siket ke janyo ciwon zuciya.

Mafi yawan labaran ba masu dadin karantawa ba ne:

  • Mutane sun shaida min iyayensu mata da suka amince shugaban Najeriya Muhammadu BUhari ya mutu tun tuni sun ce an maye gurbinsa da wani mai kama da shi dan kasar Sudan "Jubril".
  • Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya saki wani katon zaki a kan titin Moscow domin kare mutane daga karya dokar kulle da aka sanya.
  • Sarauniya Elizabeth ta bayyana a wani hoto a Burtaniya sanye da takunkumin da ya yi daidai da launin tufafinta da takalminta da kuma jakarta.

Duka labaran ana turo su ne hade da hotuna ko bidiyo.

A 'yan shekarun baya-bayan nan, samun intanet ya yi sauki a Najeriya, to wadannan tsofaffin iyayen na Najeriya yana da wahala su fahimci rudun da ke cikin hada hotunan karya da kuma cewa wadansu labaran ana yin su ne domin nishadi.

'Kamar dodo'

Kuma a mafi yawan lokuta, suna amincewa da duk wani labari da suka gani matukar da akwai hoton bidiyo a matsayin shaida.

"Mahaifiyata ta aika min hoton bidiyon wata halitta mai kamar dodo da ke tafiya sama," in ji Grace mai shekara 40, wadda ke zaune a Legas.

"Ta ce kamar yadda kuke gani cutar korona za ta bar duniyarmu."

Kari kan labaran karya:

Grace tana matukar kaduwa kan yadda kan yadda mahaifiyarta mai shekara 76 ta yarda da an dauki hoton cutar korona, wai har tana barin birnin Wuhan na China ta cikin gajimare zuwa sama.

"Ta tambaye ni yaya aka yi na san karya ne labarin sai na ce: 'Mama, cutar korona ba halittar da take tashi ba ce!'

'Ta yarda cewa ina na fi ta gaskiya kuma daga nan muka tuntsire da dariya aka kare maganar."