Amsar tambayoyinku kan Masarautar Katsinar Maradi a Nijar

 • Awwal Ahmad Janyau
 • BBC Abuja
Masarautar Maradi

Asalin hoton, Issoufou Saido Djermakoye/Facebook

Wannan maƙala ce da ta amsa tambayoyin da masu sauraro suka aiko game da tarihin Masarautar Katsinar Maraɗi a Jamhuriyyar Nijar. BBC ta yi bincike tare da tattaunawa da masana kan tushe da tarihin masarautar da kuma alaƙarta da Katsina a Najeriya.

Masarautar Katsinan Maraɗi, babbar masarauta ce mai daɗaɗɗen tarihi a Jamhuriyyar Nijar inda darajar masarautar ya tashi daga sarki zuwa Sultan.

Mafi yawancin al'ummar Masarautar Maradi Hausawa ne da kuma wasu ƙabilu na Nijar kuma ta ƙunshi Musulmi da kuma mabiya addinin Kirista.

Masarautar Maradi ta yi iyaka da yankin Damagaram daga gabas da yankin Tawa daga yamma da yankin Agadez daga arewa sannan ta yi iyaka da Najeriya daga Kudu musamman jihohin Katsina da Zamfara da Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Akan yi wa yankin Maradi kirari da gidan al'adun gargajiya na Nijar da cibiyar ilimi kuma cibiyar ciyar da ƙasa saboda harkokin kasuwanci da noman da ake yi a yankin.

BBC ta tattauna da masana tarihi, Farfesa Ado Mahaman shugaban Jami'ar Tawa a Nijar kuma masanin wanda ya yi rubuce-rubuce da dama kan Maradi da masarautar Katsinan Maradi, da kuma Issoufou Habou Magagi malamin da ke kula da gidan tarihi na jihar Maradi waɗanda suka yi ƙoƙarin amsa wasu tambayoyin da masu saurare suka aiko.

Kalmar Maradi

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Tambaya ce da mutane da dama suka aiko

Duk da ra'ayin manazarta ya bambanta kan asalin tushen kalmar Maraɗi amma masana tarihi sun ce sunan Maradi ya samo asali ne zamanin mutuimin da ya kafa garin.

Malam Issoufou Magagi mai kula da gidan Tarihi na jihar Maradi ya ce sunan Maradi ya samo asali daga kalmar "muradi" bayan Danfodio ya ci Katsina da yaƙi, lokacin da ta watse.

"Sai Ɗan Ƙasawa ya ce - mu tsaya nan kafin muradinmu ya cika mu je mu karɓe birninmu na Katsina - daga kalmar muradi aka samu sunan Maradi," in ji shi.

Ya ce sun ci gaba da zama a wurin duk da niyyar zuwa karɓo Katsina saboda sun samu ƙasa ce mai albarka ta noma da ruwa da kiwo da farauta - "bayan sun samu ƙasa mai albarka sai suka ci gaba da zama har suka dawwama a wurin."

Amma a nasa ɓangaren masanin tarihin masarautar Katsinan Farfesa Ado Mahaman ya ce sunan Maraɗi ya samo asali ne daga sarauta na wani yanki a Katsina.

Ya ce sarautar tana ƙarƙashin Katsina ne kuma wanda ke riƙe da sarautar shi ake kira "Maradi."

Ya ce akwai unguwar Maradawa da sarkin ke da ikon yankin amma kuma yana ƙarƙashin Katsina kafin jihadin Usman Danfodio.

"Sarauta ce ta ƙaramar hukuma da ke ƙarƙashin Sarkin Katsina na gidan Korau."

Tushen Masarautar Maradi da kafuwarta

Asalin hoton, Issoufou Habou Magagi

Masana tarihi sun ce Masarautar Maradi ta kafu ne tsakanin shekara 1807 - Kuma Farfesa Ado da Malam Issoufou sun ce Ɗan ƙasawa ne ya kafa Daular Katsinan Maradi.

Farfesa Ado ya ce gidan sarautar Ɗan Ƙasawa ta samo asali ne a wajajen karni na 17 daga cikin babbar Katsina. Kuma Katsinawa ne ke sarautar Maradi.

"Jikokin Korau ne Maradi, su suka kafa garin tun garin yana ƙarami suka mayar da shi babban birni da ake kira Katsinan Maradi," in ji shi.

Ya ce gidan Korou ne suka mayar da yankin Maradi cibiyar kasuwanci a Nijar - suka kuma tallafa wa jamhuriya ta farko har da turawan mallaka da kuɗin gudanarwa saboda noman gyaɗa da suke.

"Da kudin gyaɗa da kiwo suka taimaka wajen tafiyar da gwamnati har zuwa lokacin da aka samu arzikin Uranium a 1971."

Me ya sa ake cewa Sarkin Katsinan Maradi

Kamar yadda bayani ya gabata kan tushen Maradi, Masana sun ce wadanda suka gujewa jihadin Danfodio ne suka kafa Masarautar Maradi.

Kuma duk da cewa asalin Maradi wani yanki ne na ƙasar Katsina ta Najeriya, amma masarautar ta fice ne daga ƙarni na 19.

"Wasu Katsinawan Maradi a Nijar har yanzu suna ganin Katsina ta Najeriya yanki ne na masarautarsu," in ji Farfesa Ado.

Ya ce tun da Katsina ta rabu biyu, sai gidan sarautar Korau ya baro birnin Katsina ya dawo ya kafu a Maradi - "Shi ya sa ake cewa Sarkin Katsinan Maradi ko Katsina ta arewa ko katsina ta Faransa."

Issoufou Magagi ya ce Korau ne ya kafa Daular Katsina ta biyu, baya ga Daular da Komayau ya fara kafawa a karni na shida wanda ya fara kafa daular Katsinanawa a shekarar 1665.

"Muhamman Korau wanda shi ne asalin Daular Katsinan Maradi ya kafa daularsa ne a 1348. Sannan Ɗan Ƙasawa ya kafa Daular Katsinan Maradi a 1820, wacce ita ce Daular Katsinawa ta uku," in ji shi.

Farfesa Ado ya kuma ya ce Maradi tana karkashin masarautar Katsina ne tun kafin jihadi ba ma kafin zuwan turawa ba wato kafin shekara ta 1807 lokacin da goguwar jihadi ta ci Katsina.

Kamar yadda ake cewa "Katsinawa jikokin Korau - To ƴan gidan Korau ne suka taso suka dawo Maradi."

Don haka a cewar Farfesa Ado, Maradi wani yanki ne na Katsina - Kuma Maradi da Aguie da Madarounfa da Tessaoua da Dakoro da Korgom da Kanan Bakache duka yankuna ne na Katsina kafin goguwar jihadi ta raba su.

Sai dai ya ce gidan sarautar Maradi ne ya kafa Daular Katsina a karni na 15 bayan saukar Durɓawa wanda ya ba birnin Katsina kofofinta kamar kofar Ƙwaya da Ƙofar Ƙaura da Ƙofar Guga da kofar Marusa.

"Shi ne ya mayar da Katsina Sarkin Kasuwa, ya ba ta jami'o'inta kamar jami'ar Ɗan Masani da ta Ɗan Marina da ta Ƴan Doto wadda babbar jami'ia ce a Afirka duk da cewa yanzu babu ta."

Malam Issoufou Magaji ya ce ana cewa Katsinan Maradi don a bambanta da Katsina ta Najeriya wato Katsina ta ƙaya da Katsina ta Maradi ta Nijar da ake kira Katsina ta laka. Amma dukkaninsu Katsinawa ne na Nijar da Najeriya.

Kuma kowa mai cin gashin kansa ne babu wanda ke karkashin wani. Amma suna hulda ta diflomasiya da bukukuwa tsakaninsu da kuma kuma huldar zaman lafiya.

Sarakunan da suka yi mulki a Maradi

Asalin hoton, Issoufou Habou Magagi

Bayanan hoto,

Elh Mahaman Sani Kure - Buzu Dan Zambadi - Sarkin da ya fi dadewa a Masarautar Maradin Katsina

Sarakuna 23 ne suka yi mulki a Maradi. Kuma Dan Ƙasawa ne ya fara yin sarauta wanda ya fara kafa masarautar.

Sarakunan Masarautar Katsinan Maradi su ne:

 • Dan Ƙasawa 1807 zuwa 1830
 • Rauda Magajin Haladou 1830 zuwa 1836
 • Dan Mari 1836 zuwa 1843/4
 • Binoni 1843/4 zuwa 1848/9
 • Dan Mahedi 1848/9 zuwa 1851/2
 • Dan Baura 1851/2 zuwa 1852/3
 • Baskore Rauda 1852/3 zuwa 1875
 • Barmo Dan Kasawa 1875/6 zuwa 1879
 • Maza Waje Dan Kasawa 1879/8 zuwa 1882/3
 • Malam Dan Kasawa 1882/3 zuwa 1883/4
 • Salau Dan Mahedi 1883/4 zuwa 1887/8
 • Gulbi Dan KakaRauda 1887/8 zuwa 1889/90
 • Dan Dadi Binoni 1889/90 ya yi ƴan watanni
 • Mijinyawa Barmo 1889/90 zuwa 1892
 • Naibo Dan Baura 1892 zuwa 1894
 • Daci Binoni 1897 zuwa 1898
 • Kure Malam 1897/8 zuwa 1904
 • Mahaman Burja Dan Mahedi 1920 ya yi ƴan watanni
 • Ali Dan Kimale Dan Baura 1920 ya yi ƴan watanni
 • Dan kulodo Malam 1920 zuwa 1944
 • Mahaman Dan Baskore Kure 1944 zuwa 1947
 • Elh Mahaman Sani Kure - Buzu Dan Zambadi Daga 1947 zuwa 2004
 • Elh Ali Zaki - 2005 har yanzu.

Malam Issoufou Magaji ya ce Sultan na yanzu, Alhaji Ali Zaki ya hau karagar mulki a ranar 1 ga watan Oktoban 2005 kuma ya hau ne bayan rasuwar Malam Sani Kure wanda ake cewa Bouzou Dan Zambadi wanda ya hau mulki a 1947 kuma ya rasu a 2004.

"Marigayi Buzu ya shekara 57 a kan karagar mulki kuma shi ne wanda ya fi dadewa a Masarautar Katsinan Maradi," in ji shi.

Zamanin Alhaji Ali Zaki ne sarautar Katsinan Maradi ta koma Sultan tun kafa masarautar.

Asalin hoton, Issoufou Habou Magagi

Bayanan hoto,

Sultan Katsinan Maradi Elh Ali Zaki

Alakar Masarautar Katsinan Maradi da Daular Usmaniyya

Masana tarihi sun ce masarautar Maradi ba ta da danganta da Daular Usmaniyya amma sun yi gwagwarmaya daga baya ne suka shirya dab da zuwan Turawa.

Amma Malam Issoufou ya ce Daular Maradi ta yi alaka ta yaki da Daular Danfodio, "Ko da Ɗanfodio ya zo ya same su suna da addininsu na musulunci."

Ya ce Litattafan tarihi suna nuna cewa addinin musulunci ya shigo yankin Maradi a ƙarni na 11 ta hanyar kasuwanci da ke yi a yankin Sahara inda Larabawa saman Raƙuma suke fatauci tun daga Hamada su ratso yankin Katsina har zuwa Kano.

"Daga lokacin ne ƙarni na 11 ake sa ran addinin Musulunci ya shigo Daular Maradi ta hanyar labarawan da ke zuwa fatauci."

Malam Issoufou ya ce lokacin da Ɗanfodio ya zo shi yana ganin akwai kuskure kan yadda suke gudanar da addininsu wanda ya haifar da matsala tsakanin Katsinawa da Gobirawa.

"Sun yi zargin cewa Ɗanfodio ya zo ne kawai da burin fadada yankin shi - shi ne ya fake da jihadi," in ji shi.

Masanin ya ce lokacin da Usman Ɗanfodio ya tarwatsa Katsina sai ya aza Ummaru Dalaje wanda shi kuma ya tura Mani Asha zuwa yankin da yanzu ake kira Maradi

Ya ce a lokacin Katsinawan Maradi sun zargi wakilin na Ɗanfodio da azabtar da su ta hanyar sa su aikin karfi da cin zarafi.

A tarihin a cewarsa, Magaji Halidou wanda shi ne Sarki a Katsinan Maradi ya kashe kansa saboda takaicin tarwatsewar Katsina sakamakon jihadin Ɗanfodio.

Wannan ya tilasta wa Dan Ƙasawa yin gudun hijira zuwa Damagaran, daga baya kuma ya turo mayaƙansa su kashe Mani Asha kafin ya zo ya kafa daula."

"Ya tura manyan mayaƙansa ne guda shida suka yi masa juyin mulki - Suka sare kansa suka aika wa Dan ƙasawa cewa sun kashe shi kafin daga nan kuma ya dawo ya kafa Daularsa a Maradi."

Dangantakar Katsinan Maradi da Gobirawa

Asalin hoton, Issoufou Habou Magagi

Bayanan hoto,

Sultan na Gobir Elh Abdou Bala Marafa

Maradi ta kunshi Masarautu biyu masu karfi a kasar Nijar, wadanda ke da alaka ta makwabtaka duk da sun yaki juna kafin su hade kai suna yakar wanda ya kawo masu farmaki.

Farfesa Ado ya ce Katsinawa da Gobirawa makwabtaka ce tsakaninsu - suna cikin gungun manyan sarakunan Hausawa kamar Zazzau da Kano da Daura a Hausa bakwai.

Kilomita bakwai ne tsakanin Katsinan Maradi da yankin Tsibiri na Gobirawa inda jihar Maradi ta kasance mai manyan sarakuna biyu masu girman Sultan.

"Da farko Ɗan Kasawa ne ke mulki a Katsinan Maradi -Ali Dan Yakouba a Tsibiri kuma dukkanin masarautun biyu yanzu Sultan ne," in ji Malam Issoufou.

Kuma a cewarsa masarautun biyu al'adunsu da addininsu da sana'arsu duka daya - ba su da wani bambanci al'adu tsakaninsu.

Don haka kenan akwai danganta ta al'ada da addini da kuma harshe da ta kasuwanci a tsakanin Katsinawa da Gobirawa.

Farfesa Ado ya ce tun can asali Gobirawa makwabtan katsinawa ne kuma akwai wasannin dangi tsakaninsu, amma a cewarsa dalilin sarautar Gobir ne goguwar jihadi ta taso ta ci su da yaki.

Su wa ke naɗin sabon Sarki?

Bayanan hoto,

A zamanin Ali Zaki sarautar Katsinan Maradi ta koma Sultan

Masana sun ce Sarkin Katsinan Maradi Sarki ne mai cin gashin kansa amma bisa tsarin masarautar Katsinan Maradi mutum hudu ne ke zabar sabon sarki - Galadima da Ƴanɗakan Katsina da Ƙaura da Durɓi.

Yayin da wasu ke cewa daga Katsina ta Najeriya ake naɗin sarkin Katsinan Maradi, masana tarihi masarautar sun ce babu wata alaka tsakanin masu nada sarki a Katsinan Maradi ta Nijar da Katsina ta Najeriya. Kowannensu mai cin gashin kansa ne babu wanda ke karkashin wani. Amma suna hulda ta diflomasiya da bukukuwa tsakaninsu da kuma kuma huldar zaman lafiya.

Malam Issoufou ya ce Galadama da Ƴanɗakan Katsina a hannun damar Sarki suke yayin da Ƙaura da Durɓi ke hannun hagun Sarki wadanda mayakan Sarki ne.

Sannan kafin zaben sabon Sarki, suna la'akari da wasu muhimman abubuwa da suke dibawa idan Sarkin da ake son zaba ya cika darajar da ake nema.

Ana diba martabarsa da nasara - Sai an diba wanda zai faɗaɗa Daula da samar da yalwa da wadata da hayyafa ta dabbobi da jarumtaka - duk suna cikin alamomin da ake dibawa kafin nada sabon Sarki.

Hakan na nufin daga cikin ka'idojin zabar sarki - sai wanda zai kawo zaman lafiya da wadata da arziki.

Farfesa Ado Mahaman ya ce idan masu nadin Sarkin ba su jitu ba suna kiran Liman ya raba masu gardama. Kuma a cewarsa tun daga shekara ta 1445 suke zabar sarkin Katinan Maradi har zuwa yanzu.

Ya ce dukkanin masu naɗin sabon Sarkin Katsinan Maradi suna wakiltar ko wane bangare na Katsinawan Maradi daga ɓangaren bayi da gidan sarauta da sojoji da talakawa.

Sannan Farfesa ya ce ana zabar Sarkin Maradi ba bisa kama-karya ba - "Dole sai dan tsatson gidan Korau ake zaba, ba a zaben wanda ba dan gidansa ba."

Masanin Tarihin ya ce, akwai gwaji da ake yi bayan nadin sabon Sarki kuma idan bai ci gwajin ba za a fitar da shi a saka wani.

"Gwaji na farko sai ya buga Tamburra guda 12 inda yana tsakar bugawa sai Iya ta tambaye shi wane gari ya bata. amma idan ya kasa bugawa yana cikin zanzana za a cire shi a sa wani."

Za a kuma kai shi gidan Galadiman Katsina har tsawon mako daya inda za a sa shi lalle saboda Sarki mijin Kasa ne kuma Uban kasa ne."

"Sannan akwai gwaji na Mari da ake yi wa Sarki - Mai cin sarautar Mari ne zai kama habar sarki yana marinsa kadan kadan"

"Yana cewa manta da abin ake maka kana dan sarki, Manta," in ji Farfesa Ado.