George Floyd: Yadda mutuwarsa take kawo sauyi a Amurka

Democrats kneel in moment of silence for George Floyd

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yadda Nancy Pelosi da 'yan Democrat suka durkusa saboda tunawa da George Floyd

Dubban Amurkawa a jihar Texas ke jerin gwano - wata alamar girmamawa ga marigayi George Floyd - mutumin da kisan da 'yan sanda suka yi ma sa ya janyo gagarumar zanga-zanga a fadin duniya.

An kai gawarsa zuwa cocin Fountain of Praise da ke birnin Houston, birnin da Mista Floyd ya girma a cikinsa, inda mutanen birnin ke zuwa domin girmama rayuwarsa.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Lokacin da ake sauke gawar George Floyd a birnin Houston na jihar Texas gabanin a binne shi.

A lokacin da ta ke jawabi a gaban cocin, Gwen Carr - wadda danta Eric Garner ya rasa ransa a 2014 yayin da wani dan sanda ya makare shi a birnin New York ta bukaci mutanen kasar da su ci gaba da yakin neman adalci da aka fara:

"A daren da aka kashe da na, shekara shida da ta gabata, ban daina neman fafutukar neman adalci ba duk da cewa an binne shi. Abin da zan gaya wa iyalansa shi ne: kar ku daina fafutuka. Saboda abin da za su so ku yi ke nan: wato ku daina neman a yi adalci."

Ta kuma kara da cewa, "kuma ya zama dole mu hallara a nan. Mun san cewa cutar nan, wato cutar korona na nan. Amma muna da korona, kuma muna da rashin adalci."

Mutuwar Bakar fata George Floyd a hannun 'yan sanda hudu farar fata ya tayar da hankulan mutane a fadin duniya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan sandan Amurka a 2014 bayan kisan da aka yi wani bakar fata mai suna Michael Brown

Tasirin mutuwar George Floyd

Majalisar wakilan Amurka wadda 'yan jam'iyyar Democrat ke da rinjaye a cikinta ta fitar da wani daftarin doka da za ta yi wa ayyukan 'yan sanda garambawul.

Daftarin zai ba masu shigar da kara saukin tuhumar 'yan sandan da suka aikata laifukan take hakkin jama'an da ya kamata su ba kariya, kuma za ta haramta wasu dabi'u da 'yan sanda ke amfani da su kan mutane kamar shakewa da makarewa, ta kuma duba batun nuna bambancin launin fata.

A ranar Litinin, majalisar birnin Minneapolis - birnin da aka kashe George Floyd - ta kada kuri'ar rusa rundunar 'yan sandan birnin tare da yin garambawul ga dukkan ayyukan 'yan sanda.

Sai dai kawo yanzu, ba a tabbatar ko 'yan jam'iyyar Republican za su goyi bayan wannan daftarin dokar ba da ka lakaba wa sunan Justice in Policing Act of 2020 (Yin adalci a ayyukan 'yan sanda na 2020).

Shi ko Shugaba Donald tuni ya bayyana rashin amincewarsa a shafinsa na Twitter:

"Yan Democrat na son rusa rundunar 'yan sandanmu kuma suna son a yi watsi da aikinsu. Amma ni ina son a bi DOKA & ODA NE!"

Ana sa ran dan uwan marigayi George Floyd zai bayar da bahasi a wani bincike da majalisar wakilan Amurka ta shirya gudanarwa a cikin wannan makon kan yi wa ayyukan 'yan sanda garambawul.