Siyasar Edo: Obaseki ya fice daga APC

Godwin Obaseki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gwamna Obaseki ya shiga tsaka mai wuya

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya fita daga jam'iyyar APC mai mulkin kasar bayan rikicin cikin gida tsakaninsa da shugaban jam'iyyar na kasa, Adams Oshiomole.

Obaseki ya bayyanawa manema labarai bayan ganawarsa da shugaba Buhari a fadarsa da ke Abuja cewa zai koma wata jam'iyyar domin neman takara a wa'adin mulki na biyu.

A makon da ya wuce ne jam'iyyar APC ta ce Obaseki ba zai iya shiga takara a zaben fitar da gwani ba saboda a cewarta akwai bambamce-bambamce a takardun makarantarsa.

Tun lokacin da kwamitin tantance masu neman takarar gwamna na jam`iyyar APC ya tabbatar da cire shi daga cikin wadanda ya darje, Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki ya fada cikin wani mawuyacin hali irin na wanda ruwa ci shi.

Watakila wannan ne ya sa ya kasa zaune ya kasa tsaye.

'Ko PDP ce za ta yi babban kamu'

Wasu rahotanni ma na cewa ya fara wani zumuncin rana-tsaka da shugabanni da kuma jigogi a babbar jam`iyyar hamayya ta PDP da suka hada wasu gwamnoni.

Jam`iyyar APC dai ta taka wa Ambode birki, a jihar Legas, ta hana masa takara ta biyu, kuma ta kwashe nika da waka, kasancewar wanda yam aye gurbinsa, Sanwo Olu ya ci zabe. Sai dai irin wannan rikicin fidda gwanin ya kada jam`iyyar a jihohin Zamfara da Bauchi.

Abin da ba a sani ba, ko za ta kai labari idan ta sauya dan takara a jihar Edo kamar yadda ta yi a Legas. Kodayake `yan magana kan ce inda wani ya yi rawa ya samu kudi, wani in ya yi duka zai sha.

Tsohon gwamnan jihar Edo, kuma shugaban jam`iyyar APC na kasa, Adams Oshiohole shi ne ya yi uwa da makarbiya wajen zaben mista Obaseki har ya gaje shi. Amma yanzu siyasa ta raba.

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Sai da Obaseki ya gana da Buhari kafin ya bar APC

Wasu rahotanni ma na cewa tuni gwamna Obasekin ya fara kama kafar babbar jam`iyyar hamayya ta PDP ko za ta ba shi tuta don yin takara karkashin inuwarta.