Fyade a Kano: Mutumin da ya 'yi wa mai shekara 80 fyaɗe a Kano zai gurfana gaban kotu'

Bayanan sauti

An kama mutumin da ya yi wa mai shekara 80 fyade a Kano

Latsa alamar lasifika da ke sama don sauraren rahoton Khalifa Shehu Dokaji:

Rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke Arewacin Najeriya ta ce nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da mutumin nan da ta kama bisa zargin yi wa mata 40 fyade a gaban kotu.

Kakakin rundunar 'yan sandan ASP Abdul Kiyawa ya shaida wa manema labarai ranar Laraba cewa sun kama Muhammad, wanda aka sani da mai sket bayan sun dade suna farautarsa.

A cewarsa, cikin wadanda ya yi wa fyaden har da wata gyatuma mai shekara tamanin a duniya.

Ya kara da cewa mutumin -- wanda yake yi wa matan aure da 'yan mata fyade ta hanyar haura katanga domin shiga gidajensu -- ya ce shi da kansa ne yake wannan ta'ada a tare da hadin bakin wasu ba.

A cewarsa, "Da zarar mun kammala bincike a kansa za mu mika shi a gaan kotu domin ya girbe abin da ya shuka. Ya dade yana tsorata mata a garin Kwanar Dangora kuma ya ce shi yake aikatawa."

Matsalar fyade dai tana neman zama ruwan dare a Najeriya.

Ko a farkon wata yarinya mai shekara 12 ta shaida wa 'yan sanda a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya cewa wasu mutum 12 sun shafe wata biyu suna yi mata fyade.

Kazalika a farkon watan an zargi wasu mutane da kisan wata ɗaliba ƴar jami'a bayansun yi mata fyade a jihar Edo da ke kudancin Najeriya.

Masu rajin kare hakkin yara a Najeriya na ganin cewa za a ci gaba da fuskantar matsalar fyade ga kananan yara a kasar matukar gwamnati ba ta fara aiwatar da hukuncin kisa a kan masu aikata irin wannan laifi ba.