TikTok: An cire wata manhajar Zynn daga rumbun Google's Play

Da akwai manhajar Zynn a rumbun Google

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Ana ta sauke manhajar Zynn a fadin duniya tun bayan kaddamar da ita a watan jiya

Google ya cire manhajar Zynn da ake daukar hoton bidiyo daga cikin tsarinta yayin da ake tsaka da zargin manahajar da satar fasahar wasu manhajojin.

Zynn da ta saci tsarin manhajar TikTok ya sanya gasar kudi ga masu amfani da shi da suka shiga suka kalli bidiyo, cikin gaggawa ya zama daya daga cikin manhajojin da aka fi saukewa a kan waya a Amurka.

Amma ya janyo korafe-korafe daga wajen masu yawan mabiya da ke ikirarin ana kara wallafa bidiyonsu a intanet ba da izininsu ba.

Zynn ya ce ya kaddamar da sabuwar hanya ga masu amfani da shi domin su shigar da karar masu satar fasaha.

Fitacciyar manhajar dai na samun kudinta ne daga Kauishou, wani dan kasar China da ke takun saka kamfanin TikTok wanda ya mallaki byteDance.

A farkon watan Mayu ne wannan manhaja ta Zynn ta zama ta wadatu ga masu son ajiye ta kan wayoyinsu.

Haka kuma jaridar Wired ta ce mafi yawan shafukan da aka bude da suka yi satar fasaha, sun fara wallafe-wallafe ne a watan Faburairu.

Masu amfani da manhajar na samun kudi duk lokacin da suka kalli bidiyo kuma suna gayyatar abokansu su sauke manhajar.

Ana karbar kudin ne ta hanyar kyautar kati, ko kuma aika kudi ta Paypal.

Yanzu masu amfani da TikTok na korafin ana bude wasu sabbin shafuka da bayanansu a Zynn.

"A ganina abin takaici ne wannan domin kuwa satar fasaha ne, da kuma sojan gona kan bayanan mutane," Wani mai amfani da TikTok ya shaidawa Wired.

Ya kamata masu lura da harkokin kafafen "Su hana kowa wallafa abin da ba nasa ba ko kuma tura wani abu ba tare da sanin wanda ya mallake shi ba".

BBC ta tambayi Zynn kan wannan mataki na Google.

Mai magana da yawun manhajar ya ce kamfanin yana bicike kan manhajar, wadda har yanzu take kan rumbun Google.