Annobar zazzaɓin aladu 'ta kashe alade fiye da 300,000 a Nigeria'

Aladu a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Gonar aladu ta Oke Aro da ke Legas na samar wa mutum kusan 3,000 aikin yi

Wata annobar zazzaɓi ta afka wa wata katafariyar gonar kiwon aladu mai suna Oke Aro da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Wannan ne karon farko da aka tabbatar da ɓullar cutar a Najeriya cikin shekara 12.

Duk da cewa mutane ba sa kamuwa da cutar, amma takan kashe aladu masu yawa a ƙanƙanin lokaci. Hukumar Lafiyar Dabbobi ta Duniya (OIE) ta ce yiwuwar mutuwar aladun idan ta kama su zai iya kaiwa kashi 100 bisa 100.

Wani manomi ya shaida wa BBC cewa cutar ta kashe alade fiye da 300,000 tun sanda ta ɓulla a 'yan watannin da suka gabata.

"A watan Fabarairu muka lura aladu na mutuwa a wani ɓangare na gonar. Da muka gudanar da gwaji sai muka tabbatar cewa muna fuskantar cutar zazzaɓin aladu," in ji Ayo Omirin.

Gonar Oke Aro wadda ke ƙarƙashin kulawar gwamnatin Jihar Legas, ana ganin ta a matsayin ɗaya daga cikin mafiya girma a Afirka ta Yamma.

Tana samar da aikin yi ga mutum sama da 3,000 da ke fafutikar samar wa abokan hulɗa mutum miliyan 50 a yankin.