George Floyd: Hanyoyi uku na yadda ake cin zalin baƙaƙen fata a Amurka

  • Daga Tawagar Binciken Kwaf Ta
  • BBC News
Protestor holding a placard with picture of George Floyd

Asalin hoton, Getty Images

An samu rikice-rikice a fadin Amurka sakamakon kisan ɓakar fatar nan mazaunin Amurka wato George Floyd.

Mun duba wasu daga cikin alkaluma da ke da alaƙa da laifuka da shari'a a Amurka, kuma alƙaluman sun nuna irin abubuwan da baƙar fata suke fuskanta idan ana batun doka da oda.

1. Akwai yiwuwar a rinƙa kashe ɓakar fata a Amurka

Alƙaluman sun nuna adadin yadda 'yan sanda suka harbe baƙar fata, akwai yiwuwar a rinƙa kashe su idan aka kwatanyta da yawan su a Amurka.

Duk da cewa a 2019, baƙar fata su ne kashi 14 cikin 100 na yawan 'yan Amurka, su ke da kashi 23 cikin 100 na sama da mutum 1,000 da aka kashe a Amurka.

Kuma wannan adadin yana nan yadda yake tun 2017, sai dai yawan farar fata da ake kashewa ya ragu.

2. Ana yawan kama baƙar fata sakamakon shan miyagun ƙwayoyi

A 2018, cikin ko wane mutum 100,000, ana samun 750 da baƙaken fata ne waɗanda aka kama sakamakon shan miyagun ƙwayoyi, idan kuma aka kwatanta da farar fata da ake samun mutum 350 cikin 100,000.

Bincike na baya da aka gudanar kan batun shan miyagun ƙwayoyi ya nuna cewa yawan yadda ake kama farar fata sakamakon miyagun ƙwayoyi yana nan yadda yake inda kuma adadin na baƙar fata na ƙaruwa a kullum.

Misali, wani bincike da ƙungiyar American Civil Liberties ta yi ya nuna cewa akwai yiwuwar kama baƙar fata da kusan ninki 3.7 kan batun tabar wiwi idan aka kwatanta da farar fata duk da yawan yadda suke amfani da tabar wiwi ɗin duk kusan ɗaya ne.

3. An fi kai ɓakar fata fursuna

Ana kai baƙar fata gidan fursuna da kusan ninki biyar idan aka kwatanta da farar fata.

A 2018, baƙar fata ne ke da kashi 13 cikin 100 a yawan mutanen da ke Amurka, amma kuma a hakan su ke da kusan kashi uku na yawan 'yan fursuna a ƙasar.

Farar fata ke da kashi 30 cikin 100 na yawan fursunoni a Amurka - duk da cewa su ke da kashi 60 cikin 100 na yawan mutane a Amurka.

Wannan na nufin a cikin duk ɓakar fata 100,000, akan samu 1,000 da ake ke gidan fursuna, idan aka kwatanta da na farar fata da ake samun 'yan fursuna 200 cikin 100,000.

Yawan baƙar fata waɗanda ake kai wa gidan fursuna ya ragu matuƙa fiye da shekaru goma, sai dai har yanzu su ke da adadi mafi yawa na 'yan fursuna a ƙasar