Pierre Nkurunziza: Akwai rashin tabbas a Burundi bayan mutuwar shugaban ƙasa

Pierre Nkurunziza

Asalin hoton, AFP

Kwanaki kadan bayan mutuwar shugaban Burundi Pierre Nkurunziza, akwai rashin tabbas a ƙasar kan wanda zai maye gurbinsa.

Mutumin da suka ci zabe tare da Nkurunziza a matsayin mataimakinsa a zaben shugaban kasa na watan Mayu, yana jira ne a rantsar da shi a watan Agusta, amma a tsarin mulkin kasa a yanzu shugaban majalisar dokoki ne ya kamata ya zama mai riƙon ƙwarya.

Har yanzu dai babu wanda ya sha rantsuwar kama mulki.

Majalisar zartarwar kasar ta yi wani taro a ranar Alhamis ya samu jagorancin mataimakan shugaban kasa biyu. Sun tattauna kan yadda za a bi ''lamarin da ya biyo bayan mutuwar farat daya da shugaban'' ya yi, a cewar wata sanarwar da jami'ai suka fitar.

Rashin sabon shugaban kasa ya jawo zargin cewa akwai matsala a cikin jam'iyya mai mulki tsakanin zaɓaɓɓen shugaban kasar Evariste Ndayishimiye da shugaban majalisar dokokin kasar Pascal Nyabenda.

A baya can a watan Janairu, dukkansu sun nemi takarar zama shugaban kasa karkashin jam'iyyar CNDD-FDD.

Mai magana da yawun gwamnati Prosper Ntahorwamiye ya shaida wa BBC a ranar Laraba cewa za a warware halin da ake ciki a yanzu a kotu.

"Muna tuntubar kotun tsarin mulki. Tana karantar lamarin wanda zai maye gurbin shugaban kasar, zai dauki kwanaki,'' a cewarsa.

A hannu guda kuma, ana ci gaba da yada jita-jita kan mutuwar Nkurunziza.

Mutane da dama na tunanin cewa cutar korona ce ta kashe shi, amma gwamnati ta ce zuciyarsa ce ta buga.