Ranar June 12: Ana bikin zagayowar Dimokradiyya a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

A Najeriya, ranar 12 ga watan Yunin kowacce shekara ce Ranar Dimokuradiyya kuma a jawabinsa na yau, Shugaba Muhammadu Buhari ya gode wa 'yan Najeriya bisa jajircewarsu wurin kafuwar dimokuraɗiyya.

A jawabin nasa da aka yaɗa ta kafar talabijin da safiyar Juma'a, Buhari ya faɗi abubuwa da dama. Mun tsakuro muku muhimmai daga ciki:

'Yan bindiga sun yi amfani da dokar kulle a Katsina da Borno

Buhari ya ce 'yan bindiga sun yi amfani da dokar kullen da ake ciki a jihohin Katsina da Borno domin kashe mutane.

Shugaban ya miƙa ta'aziyyarsa ga waɗanda abin ya shafa amma ya nanata cewa an ci ƙarfin masu ɗauke da makamai a ƙasar.

'Annobar korona na kawo wa dimokuraɗiyyar Najeriya barazana'

Game da yaƙin da Najeriya take yi da annobar korona kuwa, Buhari ya ce annobar tana kawo wa dimokuraɗiyyar Najeriya barazana amma yana da ƙwarin gwiwar ƙasar za ta kawo ƙarshen cutar.

"Najeriya ta tsira daga rikice-rikice iri-iri a baya. Ina da ƙwarin gwiwa Najeriya za ta tsira daga wannan ma muna masu hangen nesa cikin ikon Allah."

Samar wa mutum 774,000 aikin yi

Buhari ya ce gwamnatinsa ta ɓullo da wani shiri na samar wa mutum 1,000 a kowacce ƙaramar hukuma a Najeriya a aikin yi.

Wannan yana cikin shirye-shiryen da gwamnatinsa ke yi na rage raɗaɗin da 'yan ƙasa ke ji na annobar korona.

'Na gode wa 'yan jarida kan tabbatar da dimokuraɗiyya a Najeriya'

Shugaban ya bayyana 'yan jarida a matsayin "madubin al'umma".

"Ina son na miƙa godiyata ga 'yan jarida a fafutikar tabbatar da dimokuraɗiyya tun bayan da muka samu 'yancin kai," in ji Buhari.

Ya ci gaba da cewa: "Na sani cewa ba ku fiya samun alaƙa mai kyau ba tsakaninku da gwamnatocin da suka gabata. Sai dai a bayyane take cewa ku ne madubin al'umma na ƙwarai musamman wurin sa ido kan ayyukan gwamnati."

Shuka bishiya miliyan 25

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Buhari ya ce tuni Najeriya ta fara shuka miliyoyin bishiyoyi a faɗin ƙasar.

ya ce wannan ya biyo bayan alƙawarin da ya yi a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma bishiya miliyan 25 gwamnati za ta jagoranci shukawa.

Mece ce Ranar Dimokuraɗiyya?

Wannan rana da galibin al'ummar Najeriyar suka fi sani da June 12, rana ce da tarihin kasar ba zai manta da ita ba saboda a ranar ce aka gudanar da zaben Najeriya na 1993, kodayake har kawo yanzu hukumar zaben Najeriyar ba ta sanar da wanda ya lashe shi ba.

To sai dai kuma alamu sun nuna cewa dan takarar jam'iyyar SDP, wato Moshood Kashimawo Olawale Abiola, ne ya lashe zaben inda ya kayar da abokin takararsa na jam'iyyar NRC Bashir Othman Tofa.

An dai ki sanar da sakamakon zaben ne saboda soke zaben da gwamnatin mulkin soja a karkashin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta yi.

Soke zaben dai ya janyo gagarumar tirjiya daga 'yan jam'iyyar SDP da kuma 'yan gwagwarmaya da ke da rajin kafa gwamnatin farar hula a wancan lokaci abin da ya kai ga tsare wasunsu da dama ciki har da Abiola.

Wannan rana ta 12 ga watan Yuni, ta kara karfi ne bayan da gwamnatin mulkin dimokradiyya ta zauna da kafarta a 1999.

An rinka gudanar da bikin wannan rana ne tun daga shekarar 2002, haka kuma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karawa wannan rana karfi a shekarar 2018 bayan da ya sauya ranar dimokradiyya daga ranar 29 ga watan Mayu zuwa ranar 12 ga watan Yuni.

Sauya ranar Dimokradiyya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni bai yi wa wasu 'yan Najeriyar dadi ba inda har wasu na ganin cewa siyace kawai.

A kowacce rana irin wannan gwamnatin Najeriyar kan bayar da hutu ga 'yan kasa, sannan ta shirya biki a matakin tarayya, haka suma jihohin kasar musamman na shiyyar arewa maso yammaci kan shirya irin wannan biki da nufin tunawa da ranar da aka yi zaben 12 ga watan Yuni.

A wannan karon dai za ayi bikin zagayowar wannan rana a yanayi na annobar cutar korona, abin da ake ganin bikin wannan shekarar ba zai yi armashi ba saboda yanayin da ake ciki.