Cutar korona ta hana Werner komawa Chelsea, Barca tana son dauko ‘yan wasan Tottenham da Chelsea

Timo Werner

Asalin hoton, EPA

An dakatar da shirin komawar dan wasan Jamus Timo Werner Chelsea daga RP Leipzig a kan £52m saboda dokokin killacewa da aka sanya sakamakon cutar Covid-19, abin da ya hana dan wasan mai shekara 24 yin gwaje-gwajen kiwon lafiyarsa. (The Athletic -subscription required)

Rahotanni na cewa Barcelona tana son dauko 'yan wasan baya daga Tottenham da Chelsea wadanda za ta karbo a shirin musayar da za ta bayar da Philippe Coutinho mai shekara 27. (Sport via Mail)

Ana rade radin cewa Chelsea za ta dauko dan wasan Paris St-Germain da Faransa Layvin Kurzawa. Kazalika rahotanni na cewa ita ma Arsenal tana zawarcin dan wasan mai shekara 27. (Express)

Inter Milan tana shirin sayen dan wasan Arsenal Hector Bellerin a kan £27m a bazar duk da cewa shekara uku suka ragewa dan wasan na Spaniya mai shekara 25 kafin kwangilarsa ta kare. (Express)

Dan wasan Bayern Munich Thomas Muller ya ce zai so haduwa da dan wasan Bayer Leverkusen da Jamus Kai Havertz, mai shekara 21, wanda ake rade radin zai bar Leverkusen a bazarar nan. (Metro)

Da alama dan wasan Birmingham City mai shekara 17 Jude Bellingham zai yi watsi da tayin komawa Manchester United inda zai koma Borussia Dortmund. (Sport Bild via Talksport)

Wakilin dan wasan Bayern Munich Corentin Tolisso ya yi watsi da rahotannin da ke cewa ya tattauna da Manchester United game da komawar dan wasan mai shekara 25 Old Trafford. (Standard via Sky Germany)

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Juventus da Barcelona domin yin musayar 'yan wasan tsakiya Miralem Pjanic, mai shekara 30, da Arthur Melo, mai shekara 23. (Independent)

Chelsea za ta iya sayar da dan wasan tsakiya N'Golo Kante, mai shekara 29, ga Real Madrid a bazara domin ta samu kudin musayar 'yan kwallon kafa. (Express)

Shirin da Chelsea take yi na musayar 'yan kwallon kafa a bazara ya samu tagomashi bayan da ta samu £13.5m sakamakon sayar da dan wasa mai shekara 25 Mario Pasalic ga Atalanta inda ya kwashe shekara biyu yana zaman aro. (Football London)

Wolves ta kasance kungiya ta baya bayan nan a Premier League da take son dauko dan wasan Rennes Axel Disasi, mai shekara 22 kuma tana son biyan £13.5m a kan dan wasan na Faransa. (L'Equipe - in French)

Tottenham tana ci gaba da nuna kwarin gwiwar cewa dan wasan tsakiya Eric Dier zai sabunta kwangilarsa a bazarar nan, kafin kwangilar tasa sha shiga shekarar karshe. (Football Insider)

Dan wasan Barcelona Arturo Vidal ya dage cewa yana mayar da hankalinsa kan tamaula kuma ba ya tunanin barin Nou Camp a yayin da kwantaragin dan wasan mai shekara 33 dan kasar Chilea ta shiga shekarar karshe. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Dan wasan da Arsenal take son daukowa Thomas Partey yana son ci gaba da murza leda a Atletico Madrid idan aka kara alawus dinsa a yayin da ake hasashe kan makomarsa. (Mundo Deportivo - in Spanish)