Coronavirus a Nigeria: ''Yan Najeriya kusan miliyan 40 za su rasa aikin yi saboda korona'

Osinbajo da Buhari

Asalin hoton, Nigeria Presidency

Bayanan hoto,

Kwamitin da Yemi Osinbajo ya jagoranta ya ce annobar korona ka iya raba 'yan Najeriya miliyan 39 da aikinsu

Kwamitin da aka ɗora wa alhakin samo hanyoyin farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya daga lahanin annobar korona ya ce 'yan Najeriya kusan miliyan 39.4 ne za su rasa ayyukansu nan da ƙarshen 2020 idan gwamnati ba ta ɗauki mataki ba.

Kwamitin wanda ke ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo, ya ce matakan da aka ɗauka na zaman gida sun fi shafar harkokin noma da ƙere-ƙere da kuma na yawon buɗe ido.

Ya ce raguwar kuɗin da ake samu daga man fetur za ta iya jawo wa Najeriya asarar dala miliyan 473 duk wata - kusan naira biliyan 200.

A ranar Alhamis ne kwamitin ya gabatar wa Shugaba Buhari da rahotonsa.

Daga cikin shawarwarin da ya bayar akwai fito da sabbin shirye-shirye da za su samar wa mutane ayyukan yi sannan kuma a riƙa amfani da kayan da ake ƙerawa a cikin gida a harkar noma da gine-gine da tituna.

Birnin Abuja da jihohin Legas da Ogun sun kasance cikin dokar kulle tsawon sama da wata ɗaya domin daƙile yaɗuwar cutar korona.

A ranar Alhamis aka samu adadi mafi yawa na mutanen da ke kamuwa da cutar a kullum, inda mutum 681 suka harbu.

Zuwa yanzu jumillar adadin waɗanda suka kamun sun kai 14,554, yayin da 387 suka mutu sannan 4,494 suka warke.