Coronavirus a Africa: Mutum 216,446 ne suka kamu zuwa Juma'a

Korona a Africa

Asalin hoton, CDC Africa

Bayanan hoto,

Afirka ta Kudu ce kan gaba a yawan masu cutar a Nahiyar Afirka

Hukumar CDC Africa - mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Afirka - ta ce mutum 216,446 sun kamu da cutar korona a ƙasashen Afirka 54 ya zuwa safiyar Juma'a.

Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa yanzu yankin Kudancin Afirka ya zarta na arewaci, inda ake da mutum 61,772 da suka kamu da cutar, yayin da 1,239 suka mutu da kuma 33,156 da suka warke.

Afirka ta Kudu ce kan gaba a yawan masu cutar a yankin da mutum 58,568.

A yankin arewaci kuwa, 61,615 ne suka kamu, 2,454 sun mutu sannan 26,718 sun warke. Masar ce kan gaba a yankin da mutum 39,726.

Najeriya ce ta fi saura yawan waɗanda suka harbu da cutar a Yammacin Afirka, inda take da mutum 14,554. Jumillar waɗanda suka kamu a yankin sun kai 46,433.

Mutum fiye da miliyan bakwai ne suka kamu da cutar a duniya baki ɗaya, kuma fiye da 500,000 daga cikinsu sun mutu.