Zanga-zangar Landan: Dubban mutane sun fito zanga-zanga

Protesters outside Parliament

Asalin hoton, EPA

Dubban jama'a masu zanga-zanga ne suka taru a tsakiyar Landan, duk da gargaɗin da 'yan sanda suka yi na hana zanga-zanga.

Rahotanni sun bayyana cewa an jefi 'yan sanda da kwalabe a wani wuri da ake kira Parliament Square, inda wasu rukunin jama'a ke cewa suna kare gumakan garin ne daga masu zanga-zanga kan nuna wariyar launin fata.

'Yan sanda a Landan din sun haramta wa ƙungiyoyi daban-daban zanga-zanga, biyo bayan rikice-rikicen da aka samu a makon da ya gabata.

Daga cikin zanga-zangar, akwai masu iƙirarin muhimmancin baƙar fata, wato Black Lives Matter, inda aka yi irin wannan zanga-zanga a wurare daban-daban ciki kuwa har da tsakiyar Landan.

Waɗanda suka haɗa zanga-zangar kare gumakan sun buƙaci jama'a da kada su haɗa hannu da masu zanga-zangar ƙin jinin wariyar launin fata sakamakon za a iya samun arangama da masu ra'ayin riƙau.

Sai dai wasu masu zanga-zangar sun taru a wurin tunawa da waɗanda suka yi yaƙin duniya na farko wato 'Cenotaph war memorial,' da kuma wurin da aka gina gunkin Winston Churcill a Parliament Square a ranar Asabar.

Ƙungiyoyi da dama daga faɗin ƙasar, ciki har da masu tsatsauran ra'ayi suka ce sun shigo Landan ne domin su kare tarihi.

An kewaye gunkin Winston Churcill domin kare shi daga lalatawa, tun bayan da masu zanga-zangar suka fara kirari da cewa ya kasance mai nuna wariyar launin fata lokacin da yake a raye.

Masu zanga-zangar sun rera taken Ingila inda kuma suke kiran "Ingila," duk da cewa wurin ya ɗauki ɗumi ganin cewa ga 'yan sanda a kewaye.

Asalin hoton, EPA

Ɗaya daga cikin rukunin masu zanga-zangar sun isa inda fadar Firaiminista take wato Downing Street inda suka yi wa wurin ƙawanya, amma duk da haka sai da aka rinƙa jifar 'yan sanda.

Sakatariyar harkokin cikin gida Priti Patel ta wallafa ɗaya daga cikin bidiyon arangamar da aka samu yayin zanga-zangar inda ta ce wannan "zanga-zangar ta saɓa wa doka".

"Duk wanda ya tayar da rikici ko kuma ya lalata dukiya, zai fuskanci fushin hukuma," kamar yadda ta wallafa.

"Ba za mu yarda da kai wa 'yan sandanmu hari ba."

Ta ƙara jaddada cewa cutar korona "barazana ce a garemu," ta kuma buƙaci mutane da su koma gidajensu.

Asalin hoton, EPA

'Yan sandan sun bayyana cewa sun ayyana doka mai laba 60 har sai karfe 02:00 agogon BST ranar Lahadi, inda dokar ta bayar da dama ga jami'an tsaro da su tsayar da mutane tare da yin bincike ko kuma caje su.

Cikin matakan da aka ɗauka, an buƙaci a daina zanga-zangar zuwa karfe 17:00 agogon BST a ranar Asabar.

'Yan sandan sun bayyana cewa sun ɗauki wannan mataki ne sakamakon sun samu labarin wasu za su shiga garin Landan domin su tayar da zaune tsaye.